Skip to content
Mattiyu 19:3-12

Mattiyu 19:3-12

3
Waɗansu Farisiyawa suka zo wurinsa don su gwada shi. Suka yi tambaya suka ce, “Daidai ne mutum yă saki matarsa saboda wani dalili da kuma a kan kowane dalili?”
4
Ya amsa ya ce, “Ba ku taɓa karantawa ba ne cewa, a farkon halitta, Mahalicci ‘ya yi su namiji da ta mace,’
5
ya kuma ce, ‘Saboda wannan dalili, namiji zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa yă manne wa matarsa, biyun kuwa su zama jiki guda’?
6
Ta haka, ba sa ƙara zama biyu, sai dai ɗaya. Saboda haka abin da Allah ya haɗa fa, kada mutum yă raba.”
7
Suka yi tambaya, suka ce, “To, me ya sa Musa ya umarta cewa mutum yă ba wa matarsa takardar saki, yă kuma kore ta?”
8
Yesu ya amsa ya ce, “Musa ya ba ku izini ku saki matanku saboda taurin zuciyarku ne. Amma ba haka yake ba daga farko.
9
Ina faɗa muku cewa duk wanda ya saki matarsa, sai dai a kan rashin aminci a cikin aure, ya kuwa auri wata, ya yi zina ke nan.”
10
Almajiran suka ce masa, “In haka yake tsakanin miji da mata, ashe, ya ma fi kyau kada a yi aure.”
11
Yesu ya ce, “Ba kowa ba ne zai yarda da wannan magana, sai dai waɗanda aka yarda musu.
12
Gama waɗansu bābānni ne domin haka aka haife su; waɗansu kuwa mutane ne suka mai da su haka; waɗansu kuma sun ƙi aure ne saboda mulkin sama. Duk mai iya ɗaukar wannan yă ɗauka.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options