Skip to content
Mattiyu 16:11-25

Mattiyu 16:11-25

11
Yaya kuka kāsa gane cewa ba zancen burodi nake yi ba? Sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.”
12
Sa’an nan suka gane ba cewa yake musu su yi hankali da yistin da ake amfani da shi a burodi ba ne, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da Sadukiyawa ne.
13
Sa’ad da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane suke ce da Ɗan Mutum?”
14
Suka amsa, “Waɗansu suna ce Yohanna Mai Baftisma; waɗansu kuma suna ce annabi Iliya; har wa yau waɗansu suna ce Irmiya ne ko kuma ɗaya daga cikin annabawa.”
15
Ya tambaye su, “Amma ku fa, wane ne ni a ganinku?”
16
Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Allah mai rai.”
17
Yesu ya amsa ya ce, “Mai albarka ne kai Siman ɗan Yunana, gama ba mutum ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin sama.
18
Ina kuwa gaya maka, kai ne Bitrus,a kan wannan dutse zan gina ikkilisiyata, kuma ƙofofin Hadesba za su rinjaye ta ba.
19
Zan ba ka mabuɗan mulkin sama; kome ka daure a duniya zai zama a daure a sama, kome kuma ka kunce a duniya zai zama a kunce a sama.”
20
Sa’an nan ya gargaɗe almajiransa cewa kada su faɗa wa kowa shi ne Kiristi.
21
Tun daga wannan lokaci Yesu ya fara bayyana wa almajiransa cewa dole yă tafi Urushalima yă sha wahaloli da yawa a hannun dattawa, manyan firistoci da kuma malaman dokoki, dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.
22
Bitrus ya ja shi gefe ya fara tsawata masa yana cewa, “Sam, Ubangiji! Wannan ba zai taɓa faruwa da kai ba!”
23
Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Rabu da ni, Shaiɗan! Kai abin sa tuntuɓe ne a gare ni; ba ka tunanin al’amuran Allah, sai dai al’amuran mutane.”
24
Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni.
25
Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options