Skip to content
Markus 1:21-34

Markus 1:21-34

21
Suka tafi Kafarnahum. Da ranar Asabbaci ta kewayo, sai Yesu ya shiga majami’a ya fara koyarwa.
22
Mutane suka yi mamakin koyarwarsa, domin ya koyar da su kamar wanda yake da iko, ba kamar malaman dokoki ba.
23
Nan take, sai wani mutum mai mugun ruhu a majami’arsu, ya ɗaga murya ya ce,
24
“Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki nan na Allah!”
25
Yesu ya tsawata masa ya ce, “Yi shiru! Fita daga cikinsa!”
26
Sai mugun ruhun ya jijjiga mutumin da ƙarfi, ya fita daga jikinsa da ihu.
27
Dukan mutane suka yi mamaki, suna tambayar juna suna cewa, “Mene ne haka? Tabɗi! Yau ga sabuwar koyarwa kuma da iko! Yana ma ba wa mugayen ruhohi umarni, suna kuma yin masa biyayya.”
28
Labari game da shi ya bazu nan da nan ko’ina a dukan yankin Galili.
29
Da suka bar majami’ar, sai suka tafi gidan su Siman da Andarawus, tare da Yaƙub da Yohanna.
30
Surukar Siman tana kwance da zazzaɓi, sai suka gaya wa Yesu game da ita.
31
Sai ya je wajenta, ya kama hannunta, ya ɗaga ta. Zazzaɓin kuwa ya sāke ta, ta kuma yi musu hidima.
32
A wannan yamma, bayan fāɗuwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan marasa lafiya, da masu aljanu.
33
Duk garin ya taru a ƙofar gidan.
34
Yesu kuwa ya warkar da marasa lafiya da yawa da suke da cututtuka iri-iri. Ya kuma fitar da aljanu da yawa, amma bai yarda aljanun suka yi magana ba, don sun san wane ne shi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options