Skip to content
Luka 7:25-49

Luka 7:25-49

25
In ba haka ba, to, me kuka je kallo? Mutum mai sanye da tufafi masu kyau ne? A’a, masu sa kayan tsada da suke cikin annashuwa, ai, a fada suke.
26
Amma me kuka je kallo? Annabi? I, ina kuma faɗa muku, ya ma fi annabi.
27
Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa, “ ‘Zan aiko da ɗan saƙona yă sha gabanka, wanda zai shirya hanya, a gabanka.’
28
Ina faɗa muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yohanna girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi.”
29
(Dukan mutane, har da masu karɓar haraji, da suka ji kalmomin Yesu, sai suka yarda cewa hanyar Allah gaskiya ce, domin Yohanna ne ya yi musu baftisma.
30
Amma Farisiyawa da masanan dokoki, suka ƙi nufin Allah game da su, domin Yohanna bai yi musu baftisma ba.)
31
Yesu ya ci gaba da cewa, “To, da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Kamar me suke?
32
Suna kama da yaran da suke zama a bakin kasuwa, suna kiran juna, suna cewa, “ ‘Mun busa muku sarewa, amma ba ku yi rawa ba, Mun kuma yi muku waƙar makoki, ba ku kuma yi kuka ba.’
33
Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo, ba ya cin burodi, ba ya shan ruwan inabi, sai kuka ce, ‘Ai, yana da aljani.’
34
Ɗan Mutum ya zo yana ci, yana sha, sai kuka ce, ‘Ga mai yawan ci, mashayi, da kuma abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’
35
Amma akan tabbatar da hikima ta gaskiya bisa ga dukan ’ya’yanta.”
36
To, ana nan, sai ɗaya daga cikin Farisiyawa ya gayyaci Yesu cin abincin yamma a gidansa, ya kuwa tafi gidan Bafarisiyen, ya zauna a tebur.
37
Da wata mace wadda ta yi rayuwar zunubi a wannan gari ta ji Yesu yana cin abinci a gidan Bafarisiyen, sai ta kawo ɗan tulun turaren alabasta,
38
ta kuma tsaya daga bayansa, wajen ƙafafunsa tana kuka, sai hawayenta sun fara zuba a ƙafafunsa. Sai ta goge su da gashin kanta, ta sumbace su, sa’an nan ta shafa musu turare.
39
Da Bafarisiyen da ya gayyace shi, ya ga wannan, sai ya ce a ransa, “Da mutumin nan annabi ne, da ya san ko wace ce take taɓansa, da kuma irin macen da take, cewa mai zunubi ce.”
40
Sai Yesu ya ce masa, “Siman, ina da abin da zan faɗa maka.” Shi kuwa ya ce, “Malam sai ka faɗa.”
41
Yesu ya ce, “An yi waɗansu mutum biyu da suke riƙe bashin mai ba da rance. Ana bin guda dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin.
42
Dukan biyun suka gagara biyansa, sai ya yafe musu. To, a ganinka, wa zai fi ƙaunar mutumin nan?”
43
Siman ya amsa ya ce, “A ganina, wanda aka yafe wa mai yawa ne.” Sai Yesu ya ce, “Ka faɗa daidai.”
44
Sai ya juya wajen macen, ya ce wa Siman, “Ka ga macen nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwa don ƙafafuna ba, amma ta wanke ƙafafuna da hawayenta, ta kuma goge su da gashin kanta.
45
Ba ka yi mini sumba ba, amma tun shigowata a nan, macen nan ba tă daina sumbar ƙafafuna ba.
46
Ba ka shafa mai a kaina ba, amma ta zubo turare a ƙafafuna.
47
“Saboda haka ina gaya maka, zunubanta masu yawa, an gafarta mata, gama ƙaunarta mai yawa ce. Amma wanda aka gafarta wa kaɗan kuwa, yakan nuna ƙauna kaɗan.”
48
Sai Yesu ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.”
49
Sauran baƙin suka fara ce wa juna, “Wane ne wannan, wanda har yake gafarta zunubai?”
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options