Luka 5:13-37
13
Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, “Na yarda, ka zama da tsabta!” Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi.
14
Sai Yesu ya umarce shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayu da Musa ya umarta, saboda tsarkakewarka ta zama shaida a gare su.”
15
Duk da haka, labarinsa ya ƙara bazuwa sosai, har taron mutane suka dinga zuwa don jinsa, da kuma neman warkarwa daga cututtukansu.
16
Amma Yesu sau da yawa, yakan keɓe kansa zuwa wuraren da ba kowa, yă yi addu’a.
17
Wata rana, da yake cikin koyarwa, waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki waɗanda suka zo daga kowane ƙauye a Galili, Yahudiya da Urushalima kuwa suna zaune. Ikon Ubangiji yana nan don yă warkar da masu ciwo.
18
Sai ga waɗansu mutane suka kawo wani shanyayye a kan tabarma. Suka yi ƙoƙari su shigar da shi cikin gidan, domin su kwantar da shi a gaban Yesu.
19
Da suka ga babu hanyar da za su bi saboda taron, sai suka haura rufin, suka saukar da shi a kan tabarmarsa, ta bakin ramin da suka huda a rufin, suka ajiye shi a tsakiyar taron, a gaban Yesu.
20
Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce, “Saurayi, an gafarta maka zunubanka.”
21
Farisiyawa da malaman dokoki suka fara yin tunani a zukatansu, “Wane ne wannan mutum da yake saɓo haka? Wa zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”
22
Yesu ya san abin da suke tunani, sai ya yi tambaya ya ce, “Don me kuke tunanin waɗannan abubuwa a zukatanku?
23
Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuma a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’?
24
Amma domin ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya ya gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”
25
Nan da nan, ya tashi tsaye a gabansu, ya ɗauki tabarmar da yake kwance a kai, ya tafi gida, yana yabon Allah.
26
Kowa ya yi mamaki, ya kuma yabi Allah. Suka cika da tsoro, suna cewa, “Mun ga abubuwan banmamaki yau.”
27
Bayan wannan, sai Yesu ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, yana zaune a wurin da ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.”
28
Sai Lawi ya tashi, ya bar kome da kome, ya bi shi.
29
Sai Lawi ya shirya wa Yesu wani babban liyafa a gidansa. Wani babban taron na masu karɓar haraji, tare da waɗansu suna cin abinci tare da su.
30
Amma Farisiyawa da malaman dokokin da suke a ƙungiyarsu, suka yi wa almajiransa gunaguni, suna cewa, “Don me kuke ci, kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”
31
Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya.
32
Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi zuwa ga tuba.”
33
Suka ce masa, “Almajiran Yohanna sukan yi azumi da addu’a, haka ma almajiran Farisiyawa, amma naka sai ci da sha.”
34
Yesu ya amsa ya ce, “Za ku iya sa abokan ango yin azumi yayinda yake tare da su?
35
Amma lokaci yana zuwa, da za a ɗauke ango daga gare su. A waɗancan kwanakin ne za su yi azumi.”
36
Sai ya faɗa musu wannan misali ya ce, “Ba wanda yakan yage ƙyalle daga sabuwar riga ya yi wa tsohuwar riga faci. In ya yi haka, zai yage sabuwar rigar, kuma facin daga sabuwar ba zai dace da tsohuwar rigar ba.
37
Kuma ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In ya yi haka, sabon ruwan inabi zai farfashe salkunan, ruwan inabin yă zube, salkunan kuma su lalace.
Settings