Luka 22:21-34
21
Amma hannun wanda zai ci amanata, yana cin abincin tare da ni.
22
Ɗan Mutum zai mutu kamar yadda aka ƙaddara, amma kaiton mutumin da zai bashe shi.”
23
Sai suka fara tambayar junansu, ko wane ne a cikinsu zai yi wannan.
24
Gardama ta tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma.
25
Yesu ya ce musu, “Sarakunan Al’ummai suna nuna iko a kan mutanensu, kuma waɗanda suke nuna iko a kansu, suna kiran kansu Masu Taimakon mutane.
26
Amma ku, kada ku zama haka. A maimakon haka, sai dai wanda ya fi girma a cikinku, ya zama kamar wanda ya fi ƙanƙanta, wanda kuma ke mulki, ya zama kamar mai hidima.
27
Wane ne ya fi girma? Wanda yake zaune a tebur ne, ko kuma shi da yake yin hidima? Ashe, ba wanda yake zaune a tebur ba ne? Amma ga ni, ni mai yin hidima ne a cikinku.
28
Ku ne kuka tsaya tare da ni a gwaje-gwajen da na sha.
29
Daidai kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka ni ma nake ba ku.
30
Saboda ku ci, ku sha a teburina a cikin mulkina. Kuma ku zauna a kan gadon sarauta, ku yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a.
31
“Siman, Siman, Shaiɗan ya nemi izini ya sheƙe kakamar alkama.
32
Amma na yi maka addu’a, Siman, domin kada bangaskiyarka ta kāsa. Bayan ka juyo, ka ƙarfafa ’yan’uwanka.”
33
Amma ya amsa ya ce, “Ubangiji, ina a shirye in tafi tare da kai har kurkuku, ko mutuwa ma.”
34
Yesu ya ce, “Ina gaya maka Bitrus, kafin zakara ya yi cara yau, za ka yi mūsun sanina sau uku.”
Settings