Skip to content
Luka 2:21-40

Luka 2:21-40

21
A rana ta takwas, da lokaci ya yi da za a yi masa kaciya, sai aka ba shi suna Yesu, sunan da mala’ika ya ba shi kafin a yi cikinsa.
22
Da lokacin tsarkakewarsu bisa ga Dokar Musa ya cika, sai Yusuf da Maryamu suka ɗauke shi suka haura zuwa Urushalima don su miƙa shi ga Ubangiji
23
(yadda yake a rubuce a Dokar Ubangiji cewa, “Kowane ɗan fari, za a keɓe shi ga Ubangiji”),
24
don kuma su miƙa hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Dokar Ubangiji cewa, “kurciyoyi biyu ko ’yan tattabarai biyu.”
25
To, akwai wani mutum a Urushalima mai suna Siman, shi mai adalci da kuma mai ibada. Yana jiran fansar Isra’ila, Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi.
26
An bayyana masa ta wurin Ruhu Mai Tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kiristi na Ubangiji.
27
Da Ruhu ya iza shi, sai ya shiga cikin filin haikali. Sa’ad da iyayen suka kawo jaririn nan Yesu don su yi masa abin da al’adar Doka ta bukaci,
28
sai Siman ya karɓi yaron a hannuwansa ya yabi Allah, yana cewa,
29
“Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kamar yadda ka yi alkawari, yanzu ka sallami bawanka lafiya.
30
Gama idanuna sun ga cetonka,
31
wanda ka shirya a gaban dukan mutane,
32
haske don bayyanawa ga Al’ummai da kuma ɗaukaka ga mutanenka Isra’ila.”
33
Mahaifin yaron da kuma mahaifiyarsa suka yi mamaki abin da aka faɗa game da shi.
34
Sa’an nan Siman ya sa musu albarka ya ce wa Maryamu mahaifiyarsa, “An ƙaddara yaron nan yă zama sanadin fāɗuwa da tashin mutane da yawa a Isra’ila, zai kuma zama alamar da mutane ba za su so ba,
35
ta haka za a fallasa tunanin zukatan mutane da yawa. Ke ma, takobi zai soki zuciyarki.”
36
Akwai wata annabiya ma, mai suna Anna, diyar Fanuwel, na kabilar Asher. Ta tsufa kutuf; ta yi zama da mijinta shekaru bakwai bayan sun yi aure,
37
ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da addu’a.
38
Tana haurawa wurinsu ke nan a wannan lokaci, sai ta yi wa Allah godiya ta kuma yi magana game da yaron nan ga dukan waɗanda suke sauraron fansar Urushalima.
39
Bayan da Yusuf da Maryamu suka gama yin dukan abubuwan da Dokar Ubangiji ta bukaci, sai suka koma Galili suka tafi Nazaret garinsu.
40
Yaron kuwa ya yi girma ya yi ƙarfi; ya cika da hikima, alherin Allah kuwa yana bisansa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options