Skip to content
Luka 19:39-48

Luka 19:39-48

39
Sai waɗansu Farisiyawa a cikin taron suka ce wa Yesu, “Malam, ka kwaɓi almajiranka!”
40
Ya amsa ya ce, “Ina gaya muku, ko da sun yi shiru, duwatsu za su fara kirari.”
41
Da ya yi kusa da Urushalima, ya kuma ga birnin, sai ya yi kuka a kanta,
42
kuma ya ce, “In ke, ko ke ɗin ma, dā ma kin san abin da zai kawo miki salama a wannan rana, amma yanzu an ɓoye shi daga idanunki.
43
Ranakun za su auko miki, a lokacin da abokan gābanki za su gina bango gāba da ke, su kuma kewaye inda kike, za su kuma tsare kowane gefenki, su sa ke a tsakiya.
44
Za su fyaɗa ke a ƙasa, ke da ’ya’yan da suke cikin katanganki. Ba za su bar wani dutse a kan wani ba, saboda ba ki gane da lokacin da Allah zai ziyarce ki ba.”
45
Sai ya shiga filin haikali, ya fara korar masu sayar da kaya.
46
Ya ce musu, “A rubuce, yake cewa, ‘Gidana, zai zama gidan addu’a,’amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ”
47
Kowace rana, ya yi ta koyarwa a haikalin. Amma manyan firistoci, da malaman dokoki, da shugabannin mutane, suna ƙoƙarin kashe shi.
48
Amma ba su sami hanyar yin haka ba, domin kalmominsa sun kama hankalin dukan mutanen.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options