Luka 12:35-53
35
“Ku shirya ɗamara don hidima. Ku bar fitilunku suna ci,
36
kamar maza da suke jiran maigidansu ya dawo daga bikin aure. Saboda duk lokacin da ya dawo ya ƙwanƙwasa ƙofa, a shirye suke su buɗe masa nan da nan.
37
Zai zama da albarka in maigida ya dawo, ya tarar da bayinsa suna zaman tsaro. Gaskiya ni faɗa muku, zai sa kayan hidima da kansa, ya sa bayinsa su zauna kan tebur, sa’an nan ya yi musu hidimar abinci.
38
Zai zama da albarka ga bayin da maigidansu ya iske su, suna zaman tsaro, a duk lokacin da ya dawo, ko da ya dawo a sa’a ta biyu, ko ta uku na tsakar dare ne.
39
Amma ku fahimci wannan. Da maigida ya san sa’ar da ɓarawo zai zo, ai, da ba zai bari a shiga, a fasa masa gida ba.
40
Ku ma, sai ku zauna da shiri, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku yi tsammani ba.”
41
Bitrus ya yi tambaya ya ce, “Ya Ubangiji, mu ne kake faɗa wa wannan misali, ko kuwa ga kowa da kowa ne?”
42
Ubangiji ya amsa ya ce, “To, wane ne manaja mai aminci da hikima, wanda maigida ya ba shi riƙon bayinsa, domin ya ba su abincinsu a daidai lokaci?
43
Zai zama da albarka ga bawan nan wanda maigidan ya dawo, ya same shi yana yin haka.
44
Gaskiya nake gaya muku, maigidan zai ba shi riƙon dukan dukiyarsa.
45
Amma da a ce bawan ya yi tunani a zuciyarsa ya ce, ‘Ai, maigidana ya yi jinkirin dawowa,’ sa’an nan ya fara dūkan bayin, maza da mata, ya kuma shiga ci, da sha, har da buguwa.
46
Maigidan bawan nan zai dawo a ranar da wannan bawan bai yi tsammaninsa ba, kuma a sa’ar da bai sani ba. Maigidan zai yayyanka shi, ya kuma ba shi rabonsa tare da marasa bangaskiya.
47
“Bawan da ya san nufin maigidansa, kuma bai yi shiri ba, ko kuma bai yi abin da maigidansa yake so ba, zai sha mummunan duka.
48
Amma wanda bai sani ba, ya kuwa yi abin da ya isa horo, za a dūke shi kaɗan. Duk wanda aka ba shi mai yawa, mai yawan ne za a bida daga gare shi. Duk wanda kuma aka ba shi riƙon amana mai yawa, fiye da haka kuma za a bida daga gare shi.
49
“Na zo ne domin in kawo wuta a duniya. Ina so da ta riga ta ƙunu!
50
Amma ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa damu sosai, sai na kammala ta!
51
Kuna tsammani na zo domin in kawo salama a duniya ne? A’a! Ina gaya muku, rabuwa ne.
52
Daga yanzu, za a iske mutum biyar a gida ɗaya sun rabu, suna gāba da juna, uku suna gāba da biyu, biyun suna gāba da ukun.
53
Za su rarrabu. Mahaifi yana gāba da ɗan, ɗan kuma yana gāba da mahaifin. Mahaifiya tana gāba da diyar, diyar kuma tana gāba da mahaifiyar. Suruka tana gāba da matar ɗa, matar ɗa kuma tana gāba da suruka.”
Settings