Skip to content
Luka 12:13-34

Luka 12:13-34

13
Sai wani mutum daga cikin taron ya ce masa, “Malam, ka ce wa ɗan’uwana ya raba gādon da ni.”
14
Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai, wa ya naɗa ni alƙali, ko mai sulhu a tsakaninku?”
15
Sai ya ce musu, “Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba.”
16
Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai.
17
Ya yi tunani a ransa ya ce, ‘Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?’
18
“Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki.
19
Ni kuma zan ce wa raina, “Kana da kaya da yawa masu kyau, da aka yi ajiyarsu domin shekaru da dama masu zuwa. Yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa.” ’
20
“Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za a nemi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?’
21
“Haka zai zama ga duk wanda ya tara wa kansa dukiya, amma ba shi da arziki a gaban Allah.”
22
Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Saboda haka, ina faɗa muku, kada ku damu game da rayuwarku, abin da za ku ci, ko kuma game da jikinku, abin da za ku yafa.
23
Rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi.
24
Ku dubi hankaki. Ba sa shuki ko girbi, kuma ba su da ɗakin ajiya ko rumbu ba, duk da haka, duk da haka, Allah na ciyar da su. Darajarku ta fi na tsuntsaye sau da yawa!
25
Wane ne a cikinku ta wurin damuwarsa, zai iya ƙara ko sa’a ɗaya ga rayuwarsa?
26
Tun da ba za ku iya yin wannan ƙanƙanin abu ba, me ya sa kuke damuwa a kan sauran?
27
“Ku dubi yadda furanni suke girma. Ba sukan yi aiki, ko saƙa ba, duk da haka, ina faɗa muku cewa, ko Solomon cikin kyakkyawan darajarsa duka, bai yafa kayan ado da ya kai kamar na ko ɗaya a cikinsu ba.
28
In haka ne Allah yake yi wa ciyayin jeji sutura, wadda yau suna nan, sa’an nan gobe kuma a jefa cikin wuta, Allah ba zai yi muku sutura fiye da ciyayin jeji ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya!
29
Kada ku sa zuciyarku a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada ku damu a kan su.
30
Gama duniya da ba tă san Allah ba, tana faman neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa, ya san kuna bukatarsu.
31
Amma ku nemi mulkinsa, za a kuwa ƙara muku waɗannan abubuwa.
32
“Ya ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, gama ya gamshi Ubanku ya ba ku mulkin.
33
Ku sayar da dukiyarku, ku ba wa matalauta. Ku yi wa kanku jakar kuɗin da ba za su lalace ba. Ku yi wa kanku ajiyar dukiyar da ba za tă kare ba a sama, inda ɓarawo ba zai yi kusa ba, asu kuma ba za su iya su lalatar ba.
34
Gama inda dukiyarku take, nan ne zuciyarku ma take.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options