Luka 12:1-12
1
Ana nan sa’ad da taron dubban mutane suka taru har suna tattaka juna, Yesu fara yin magana, da farko da almajiransa ya ce, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato, munafunci.
2
Ba abin da yake rufe da ba za a fallasa ba, ko kuma abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba.
3
Abin da kuka faɗa a cikin duhu, za a ji shi a hasken rana. Kuma abin da kuka faɗa a kunne, a cikin ɗakunan ciki-ciki, za a yi shelarsa daga kan rufin ɗakuna.
4
“Ina dai gaya muku abokaina, kada ku ji tsoron masu kashe jiki, amma bayan haka, ba sauran abin da za su iya yi.
5
Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron wanda, bayan da ya kashe jikin, yana da iko ya jefa ku cikin jahannama ta wuta. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa.
6
Ba ana sayar da kanari biyar a kan kobo biyu ba? Duk da haka, Allah bai manta da ko ɗayansu ba.
7
Tabbatacce, gashin kanku ɗin nan ma, an ƙidaya su duka. Kada ku ji tsoro. Darajarku ta fi na kanari masu yawa girma.
8
“Ina gaya muku, duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai shaida shi a gaban mala’ikun Allah.
9
Amma wanda ya yi mūsun sanina a gaban mutane, shi ma za a yi mūsunsa a gaban mala’ikun Allah.
10
Kuma duk wanda ya faɗi kalmar zagi a kan Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya saɓa wa Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba.
11
“Sa’ad da an kai ku a gaban majami’u, da gaban masu mulki, da kuma gaban masu iko, kada ku damu da yadda za ku kāre kanku, ko kuma abin da za ku faɗa,
12
gama Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya dace ku faɗa a lokacin.”
Settings