Yoshuwa 17:6-13
6
domin ’ya’ya mata na kabilar Manasse sun sami gādo tare da ’ya’ya maza. Aka ba wa sauran mutanen kabilar Manasse ƙasar Gileyad.
7
Iyakar ƙasar Manasse ta tashi daga Asher zuwa Mikmetat a gabashin Shekem. Iyakar kuma ta miƙe har zuwa kudu wadda ta ƙunshi mutanen da suke zaune a En Taffuwa.
8
(Manasse ne yake da ƙasar Taffuwa, amma garin Taffuwa kansa, a kan iyakar Manasse ta mutanen Efraim ce.)
9
Sa’an nan iyakar ta ci gaba ta yi kudu zuwa Rafin Kana. Akwai garuruwan da suke kudancin rafin, waɗanda suke Efraim, ko da yake suna cikin yankin Manasse. Iyakar Manasse ta miƙe zuwa arewa ta bi gefen rafin ta kuma ƙarasa a Bahar Rum.
10
Ƙasar a wajen kudu ta Efraim ce, ta wajen arewa kuma ta Manasse ce. Bahar Rum ita ce iyakarsu. Asher yana wajen arewa, Issakar kuma a wajen gabas.
11
A yanki tsakanin Issakar da Asher, Manasse yana da waɗannan wurare, Bet-Sheyan, Ibileyam da ƙauyukanta, da mazaunan Dor da ƙauyukanta, da mazaunan En Dor da ƙauyukanta, da mazaunan Ta’anak da ƙauyukanta, da mazaunan Megiddo da ƙauyukanta (Na uku cikin jerin shi ne Nafot).
12
Duk da haka mutanen Manasse ba su iya mallakar garuruwan nan ba, domin Kan’aniyawa sun nace da zama a wannan yanki.
13
Da Isra’ilawa suka yi ƙarfi, sai suka sa Kan’aniyawa suka zama masu yin musu aiki, amma ba su iya korarsu duka ba.
Settings