Skip to content
Yohanna 12:20-36

Yohanna 12:20-36

20
To, akwai waɗansu Hellenawa a cikin waɗanda suka haura don su yi sujada a Bikin.
21
Suka zo wurin Filibus, wanda yake daga Betsaida ta Galili, da roƙo. Suka ce, “Ranka yă daɗe, muna so mu ga Yesu.”
22
Sai Filibus ya je ya gaya wa Andarawus, Andarawus da kuma Filibus suka gaya wa Yesu.
23
Yesu ya amsa ya ce, “Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum.
24
Gaskiya nake gaya muku, sai ƙwayar alkama ta fāɗi ƙasa ta mutu, in ba haka ba za tă kasance ƙwaya ɗaya tak. Amma in ta mutu, za tă ba da ’ya’ya da yawa.
25
Duk mai ƙaunar ransa, zai rasa shi, duk mai ƙin ransa a wannan duniya, zai kiyaye shi har yă zuwa rai madawwami.
26
Duk wanda zai bauta mini dole yă bi ni, inda kuma nake, a can bawana zai kasance. Ubana zai girmama wanda yake bauta mini.
27
“Yanzu kuwa na damu, amma me zan ce? ‘Uba, ka cece ni daga wannan sa’a’? A’a, ai, saboda wannan dalili ne musamman na zo.
28
Uba, ka ɗaukaka sunanka!” Sai wata murya ta fito daga sama ta ce, “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi.”
29
Taron da suke a wurin suka ji, suka ce an yi tsawa; waɗansu kuwa suka ce mala’ika ne ya yi masa magana.
30
Yesu ya ce, “An yi wannan muryar saboda amfaninku ne, ba don nawa ba.
31
Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shari’a, yanzu ne za a tumɓuke mai mulkin duniyan nan.
32
Amma ni, sa’ad da aka ɗaga ni daga ƙasa, zan ja dukan mutane gare ni.”
33
Ya faɗa haka ne don yă nuna irin mutuwar da zai yi.
34
Sai taron suka ce, “Ahab, Dokarmu ta gaya mana cewa, Kiristi zai kasance har abada, to, yaya za ka ce, ‘Dole ne a ɗaga Ɗan Mutum?’ Wane ne wannan ‘Ɗan Mutum’?”
35
Sai Yesu ya ce musu, “Haske zai kasance da ku na ɗan lokaci. Ku yi tafiya yayinda hasken yana nan tare da ku, kada duhu yă cim muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda za shi ba.
36
Ku dogara ga hasken yayinda kuke da shi, don ku zama ’ya’yan haske.” Da Yesu ya gama magana, sai ya tafi ya ɓuya daga gare su.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options