Skip to content
Ayuba 6:1-13

Ayuba 6:1-13

1
Sa’an nan Ayuba ya amsa,
2
“Da kawai za a iya auna wahalata a kuma sa ɓacin raina a ma’auni!
3
Ba shakka da sun fi yashin teku nauyi, shi ya sa nake magana haka.
4
Kibiyoyin Maɗaukaki suna a kaina, ruhuna yana shan dafinsa; fushin Allah ya sauka a kaina.
5
Jaki yakan yi kuka sa’ad da ya sami ciyawar ci, ko saniya takan yi kuka in ta sami abincinta?
6
Akan cin abinci marar ɗanɗano ba tare da an sa gishiri ba, ko akwai wani ƙanshin daɗi a cikin farin ruwan ƙwai?
7
Na ƙi in taɓa shi; irin wannan abinci zai sa ni rashin lafiya.
8
“Kash, da ma Allah zai ba ni abin da nake fatar samu, da ma Allah zai biya mini bukatata,
9
wato, Allah yă kashe ni, yă miƙa hannunsa yă yanke raina!
10
Da sai in ji daɗi duk zafin da nake sha ban hana maganar Mai Tsarkin nan cika ba.
11
“Wane ƙarfi nake da shi, har da zan ci gaba da sa zuciya? Wane sa zuciya ne zai sa in yi haƙuri?
12
Da ƙarfin dutse aka yi ni ne? Ko jikina tagulla ne?
13
Ina da wani ikon da zan iya taimakon kai na ne, yanzu da aka kore nasara daga gare ni?
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options