Ayuba 6:1-7
1
Sa’an nan Ayuba ya amsa,
2
“Da kawai za a iya auna wahalata a kuma sa ɓacin raina a ma’auni!
3
Ba shakka da sun fi yashin teku nauyi, shi ya sa nake magana haka.
4
Kibiyoyin Maɗaukaki suna a kaina, ruhuna yana shan dafinsa; fushin Allah ya sauka a kaina.
5
Jaki yakan yi kuka sa’ad da ya sami ciyawar ci, ko saniya takan yi kuka in ta sami abincinta?
6
Akan cin abinci marar ɗanɗano ba tare da an sa gishiri ba, ko akwai wani ƙanshin daɗi a cikin farin ruwan ƙwai?
7
Na ƙi in taɓa shi; irin wannan abinci zai sa ni rashin lafiya.
Settings