Ayuba 37:1-11
1
“Wannan ya sa gabana ya fāɗi, zuciyata ta yi tsalle.
2
Ka saurara! Ka saurari rurin muryarsa, tsawar da take fita daga bakinsa.
3
Ya saki walƙiyarsa, a ƙarƙashin dukan sammai ya kuma aika ta ko’ina a cikin duniya.
4
Bayan wannan sai ƙarar rurinsa ta biyo; Ya tsawata da muryarsa mai girma. Sa’ad da ya sāke yin tsawa ba ya rage wani abu.
5
Muryar Allah tana tsawatawa a hanyoyi masu ban al’ajabi; yana yin manyan abubuwa waɗanda sun wuce ganewarmu.
6
Yakan ce wa dusar ƙanƙara, ‘Fāɗo a kan duniya,’ ya kuma ce wa ruwa, ‘Zubo da ƙarfi.’
7
Domin dukan mutanen da ya halitta za su san aikinsa, ya hana kowane mutum yin wahalar aiki.
8
Dabbobi sun ɓoye; sun zauna cikin kogunansu.
9
Guguwa tana fitowa daga inda take, sanyi kuma daga iska mai sanyi.
10
Da numfashinsa Allah yana samar da ƙanƙara sai manyan ruwaye su zama ƙanƙara.
11
Yana cika gizagizai da lema; yana baza walƙiyarsa ta cikinsu.
Settings