Ayuba 36:22-33
22
“An ɗaukaka Allah cikin ikonsa. Wane ne malami kamar sa?
23
Wane ne ya nuna masa hanyar da zai bi, ko kuma wane ne ya ce masa, ‘Ba ka yi daidai ba?’
24
Ka tuna ka ɗaukaka aikinsa, waɗanda mutane suka yaba a cikin waƙa.
25
Dukan ’yan adam sun gani; mutane sun hanga daga nesa.
26
Allah mai girma ne, ya wuce ganewarmu! Yawan shekarunsa ba su bincikuwa.
27
“Yana sa ruwa yă zama tururi yă zubo daga sama.
28
Gizagizai suna zubo da raɓarsu kuma ruwan sama yana zubowa ’yan adam a wadace.
29
Wane ne zai iya gane yadda ya shimfiɗa gizagizai yadda yake tsawa daga wurin zamansa?
30
Dubi yadda ya baza walƙiyarsa kewaye da shi, tana haskaka zurfin teku.
31
Haka yake mulkin al’ummai yana kuma tanada abinci a wadace.
32
Yana cika hannuwansa da walƙiya kuma yana ba ta umarni tă fāɗi a inda ya yi nufi.
33
Tsawarsa tana nuna cewa babbar iska da ruwa suna zuwa; ko shanu sun san da zuwansa.
Settings