Skip to content
Ayuba 31:19-34

Ayuba 31:19-34

19
In da na ga wani yana mutuwa don rashin sutura, ko wani mai bukata da ba shi da riga,
20
kuma zuciyarsa ba tă gode mini ba don na yi masa sutura da gashin tumakina,
21
in na ɗaga hannuna don in cuci maraya, domin na san in na faɗa za a ji ni a wurin masu shari’a,
22
bari hannuna yă guntule daga kafaɗata, bari yă tsinke daga inda aka haɗa shi.
23
Gama ina jin tsoron hallaka daga Allah, kuma domin tsoron ɗaukakarsa ba zan iya yin waɗannan abubuwa ba.
24
“In na dogara ga zinariya ko kuma na ce wa zallan zinariya, ‘Gare ki nake dogara,’
25
in na yi fahariya don yawan dukiyata, arzikin da hannuwana suka samu.
26
In na dubi rana cikin haskenta, ko kuma wata yana tafiyarsa,
27
zuciyata ta jarrabtu gare su a ɓoye, hannuna kuma ya sumbace su.
28
Waɗannan ma za su zama zunubin da za a shari’anta ke nan don zai zama na yi wa Allah na sama rashin aminci.
29
“In na yi murna domin mugun abu ya faru da maƙiyina; ko kuma domin wahala ta same shi,
30
ban bar bakina yă yi zunubi ta wurin la’anta shi ba,
31
in mutanen gidana ba su taɓa cewa, ‘Wane ne bai ƙoshi da naman Ayuba ba?’
32
Ba baƙon da ya taɓa kwana a titi, gama koyaushe ƙofata tana buɗe domin matafiya,
33
in na ɓoye zunubina yadda mutane suke yi, ta wurin ɓoye laifina a cikin zuciyata,
34
domin ina tsoron taron mutane kuma ina tsoron wulaƙancin da dangina za su yi mini, sai na yi shiru kuma ban fita waje ba.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options