Skip to content
Ayuba 31:16-23

Ayuba 31:16-23

16
“In na hana wa matalauta abin da suke so, ko kuma in sa idanun gwauruwa su yi nauyi don kuka,
17
in na ajiye burodina don kaina kaɗai, ban kuwa ba wa marayu abinci sa’ad da suke jin yunwa,
18
amma tun suna tasowa na lura da su, kamar yadda mahaifi zai lura da ɗa, kuma tun da aka haife ni ina lura da gwauruwa.
19
In da na ga wani yana mutuwa don rashin sutura, ko wani mai bukata da ba shi da riga,
20
kuma zuciyarsa ba tă gode mini ba don na yi masa sutura da gashin tumakina,
21
in na ɗaga hannuna don in cuci maraya, domin na san in na faɗa za a ji ni a wurin masu shari’a,
22
bari hannuna yă guntule daga kafaɗata, bari yă tsinke daga inda aka haɗa shi.
23
Gama ina jin tsoron hallaka daga Allah, kuma domin tsoron ɗaukakarsa ba zan iya yin waɗannan abubuwa ba.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options