Skip to content
Irmiya 40:1-7

Irmiya 40:1-7

1
Sai magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji bayan Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya sake shi a Rama. Ya sami Irmiya a daure da sarƙoƙi a cikin sauran kamammu daga Urushalima da kuma Yahuda waɗanda ake kaiwa zaman bauta a Babilon.
2
Sa’ad da shugaban matsaran ya sami Irmiya sai ya ce masa, “Ubangiji Allahnka ya sa wannan masifa saboda wannan wuri.
3
Yanzu kuma Ubangiji ya cika shi; ya yi kamar yadda ya faɗa. Dukan wannan ya faru domin kun yi zunubi ga Ubangiji ba ku kuwa yi masa biyayya ba.
4
Amma yau ina ’yantar da kai daga sarƙoƙin da suke a hannuwanka. Zo mu tafi Babilon, in kana so, zan kuwa lura da kai; amma in ba ka so, kada ka zo. Ga shi, dukan ƙasar tana a gabanka; ka tafi duk inda ka so.”
5
Amma, kafin Irmiya yă juya yă tafi, Nebuzaradan ya ƙara da cewa, “Ka koma wurin Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, wanda sarkin Babilon ya naɗa a kan garuruwan Yahuda, ka zauna da shi a cikin mutane, ko kuwa ka tafi duk inda ka ga dama.” Sa’an nan shugaban ya ba shi abinci da kuma kyauta sai ya bar shi ya tafi.
6
Saboda haka Irmiya ya tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam, a Mizfa ya zauna tare da shi a cikin mutanen da aka bari a ƙasar.
7
Sa’ad da dukan shugabannin hafsoshin tare da mutanen da suke a karkara suka ji cewa sarkin Babilon ya naɗa Gedaliya ɗan Ahikam gwamna a kan ƙasar ya kuma sa shi ya lura da maza, mata da ’ya’yan da suke mafi talauci a ƙasar da waɗanda ba a kwashe zuwa zaman bauta a Babilon ba,
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options