Skip to content
Irmiya 40:7-12

Irmiya 40:7-12

7
Sa’ad da dukan shugabannin hafsoshin tare da mutanen da suke a karkara suka ji cewa sarkin Babilon ya naɗa Gedaliya ɗan Ahikam gwamna a kan ƙasar ya kuma sa shi ya lura da maza, mata da ’ya’yan da suke mafi talauci a ƙasar da waɗanda ba a kwashe zuwa zaman bauta a Babilon ba,
8
sai suka zo wurin Gedaliya a Mizfa, Ishmayel ɗan Netaniya, Yohanan da Yonatan ’ya’yan Kareya, da Serahiya ɗan Tanhumet maza, ’ya’yan Efai maza, mutumin Netofa, da Yezaniya ɗan mutumin Ma’aka da mutanensu.
9
Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, ya yi rantsuwa don yă tabbatar musu da mutanensu. Ya ce, “Kada ku ji tsoron bauta wa Babiloniyawa. Ku zauna a ƙasar ku bauta wa sarkin Babilon, zai kuma yi muku amfani.
10
Ni kaina zan zauna a Mizfa in zama wakilinku a gaban Babiloniyawa waɗanda za su zo wurinmu, amma ku girbe ruwan inabi, ’ya’yan itatuwa na kaka, da mai, ku zuba su a tulunan ajiyarku, ku kuma zauna a garuruwan da kuka ci.”
11
Sa’ad da dukan Yahudawan da suke a Mowab, Ammon, Edom da sauran ƙasashe suka ji cewa sarkin Babilon ya bar raguwa a Yahuda ya kuma naɗa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan gwamna a kansu,
12
sai suka dawo ƙasar Yahuda, wurin Gedaliya a Mizfa, daga dukan ƙasashen da suke a warwatse. Suka girbe ruwan inabi a yalwace da ’ya’yan itatuwan kaka.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options