Irmiya 32:26-44
26
Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,
27
“Ni ne Ubangiji Allah na dukan ’yan adam. Akwai wani abin da ya gagare ni?
28
Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, ina gab da ba da wannan birni ga Babiloniyawa da kuma ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, wanda zai yaƙe ta.
29
Babiloniyawan da suke yaƙi da wannan birni za su zo ciki su cinna masa wuta; tare da gidaje inda mutane suka tsokane ni na yi fushi ta wurin ƙona turare a rufin ɗakuna wa Ba’al suka zub da hadayun sha wa waɗansu alloli.
30
“Mutanen Isra’ila da na Yahuda ba abin da suka yi sai mugunta a gabana daga ƙuruciyarsu; tabbatacce, mutanen Isra’ila ba su yi kome ba sai dai tsokane ni da abin da hannuwansu suka yi, in ji Ubangiji.
31
Daga ranar da aka gina ta har zuwa yanzu, wannan birni ta tā da fushina da hasalata da dole a kawar da ita daga gabana.
32
Mutanen Isra’ila da na Yahuda sun tsokane ni ta wurin dukan muguntar da suka aikata su, sarakunansu da fadawansu, firistocinsu da annabawa, mutanen Yahuda da mutanen Urushalima.
33
Sun juya mini bayansu ba fuskokinsu ba; ko da yake na koyar da su sau da sau, ba su saurara ko bi horo na ba.
34
Sun kafa gumakansu na banƙyama a cikin haikalina wanda ake kira da sunana, sun kuwa ƙazantar da shi.
35
Sun gina masujadai kan tudu wa Ba’al a Kwarin Ben Hinnom don su miƙa ’ya’yansu maza da mata hadaya ga Molek, ko da yake ban taɓa umarce su ba, bai kuma zo mini cewa su yi abin banƙyama irin wannan ba ta haka suka sa Yahuda ya yi zunubi.
36
“Kana cewa game da wannan birni, ‘Ta wurin takobi, yunwa da annoba za a ba da shi ga sarkin Babilon’; amma ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa
37
tabbatacce zan tattara su daga dukan ƙasashen da na kore su zuwa cikin fushina da hasalata mai girma; zan komo da su wurin nan in sa su zauna lafiya.
38
Za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu.
39
Zan ba su zuciya ɗaya da aiki ɗaya, don kullum su ji tsorona domin amfaninsu da kuma amfanin ’ya’yansu a bayansu.
40
Zan yi madawwamin alkawari da su. Ba zan taɓa barin aikata musu alheri ba, zan kuma iza su su ji tsorona, don kada su ƙara juya daga gare ni.
41
Zan yi farin ciki a yin musu alheri, tabbatacce zan su dasa a wannan ƙasa da dukan zuciyata da dukan raina.
42
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, yadda na kawo dukan wannan masifa a kan wannan mutane, haka zan ba su wadatar da na yi musu alkawari.
43
Za a sāke sayi filaye a wannan ƙasa da kuka ce, ‘Kango ce, ba mutane ko dabbobi, gama an ba da ita ga Babiloniyawa.’
44
Za a sayi filaye da azurfa, a kuma sa hannu a takardan ciniki, a liƙe a kuma shaida a yankin Benyamin, a ƙauyukan kewayen Urushalima, a garuruwan Yahuda da kuma a garuruwan ƙasar tudu, na yammancin gindin dutse da na Negeb, domin zan maido da wadatarsu, in ji Ubangiji.”
Settings