Irmiya 32:16-25
16
“Bayan na ba da takardun ciniki ga Baruk ɗan Neriya, sai na yi addu’a ga Ubangiji na ce,
17
“A, Ubangiji Mai Iko Duka, ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka mai girma da kuma hannunka mai iko. Ba abin da ya gagare ka.
18
Kakan nuna ƙauna ga dubbai amma kakan hukunta ’ya’ya saboda laifin ubanninsu a bayansu. Ya mai girma da kuma Allah mai iko, wanda sunansa ne Ubangiji Maɗaukaki,
19
manufofinka da girma suke, ayyukanka kuma masu girma ne. Idanunka suna a buɗe ga dukan hanyoyin mutane; kakan sāka wa kowa gwargwadon halinsa yadda ya dace.
20
Ka aikata ayyukan banmamaki da kuma al’ajabai a Masar ka kuma ci gaba da su har yă zuwa yau, a Isra’ila da kuma a cikin dukan ’yan adam, ka kuma sami sunan da har yanzu yake naka.
21
Ka fitar da mutanenka Isra’ila daga Masar da alamu da abubuwa banmamaki, ta wurin hannu mai iko da kuma hannu mai ƙarfi tare da banrazana mai girma.
22
Ka ba su wannan ƙasa da ka rantse za ka ba wa kakanni kakanninsu, ƙasa mai zub da madara da zuma.
23
Suka shiga suka mallake ta, amma ba su yi maka biyayya ba, ba su kuma bi dokarka ba; ba su yi abin da ka umarce su ba. Saboda haka ka kawo masifa a kansu.
24
“Duba yadda aka gina mahaurai don a kame birni. Saboda takobi, yunwa da annoba, za a ba da birnin ga Babiloniyawa waɗanda suka kewaye shi da yaƙi. Abin da ka faɗa ya faru, yadda kake gani yanzu.
25
Ko da yake za a ba da birnin ga Babiloniyawa, kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka ce mini, ‘Saye fili da azurfa ka kuma sa a shaida cinikin.’ ”
Settings