Ishaya 44:6-20
6
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, Sarki da kuma Mai Fansar Isra’ila, Ubangiji Maɗaukaki. Ni ne farko ni ne kuma ƙarshe; in ban da ni babu wani Allah.
7
Wane ne kuwa kama da ni? Ya faɗa a ji. Bari yă yi shela ya kuma nuna shi a gabana mene ne ya faru tun da na kafa mutanena na dā, mene ne kuma bai riga ya faru ba, I, bari yă faɗa abin da zai zo.
8
Kada ku firgita kada kuma ku ji tsoro. Ban furta wannan na kuma yi faɗar haka tuntuni ba? Ku ne shaiduna. Akwai wani Allah in ban da ni? A’a, babu wani Dutse; ban san da wani ba.”
9
Duk masu yin gumaka ba kome ba ne, da kuma abubuwan da suke ɗauka da daraja banza ne. Waɗanda za su yi magana a madadinsu makafi ne; jahilai ne, marasa kunya.
10
Waɗanda suke siffanta allah su kuma yi zubin gunki, waɗanda ba za su yi musu ribar kome ba?
11
Shi da irinsa za su sha kunya; masu sassaƙa ba kome ba mutane ne kurum. Bari su tattaru su ɗauki matsayinsu; za su firgita su kuma sha mummunan kunya.
12
Maƙeri yakan ɗauki kayan aiki ya yi aiki da shi a cikin garwashi; ya ƙera gunki da guduma, ya gyara shi da hannuwansa masu ƙarfi. Yakan ji yunwa ya kuma rasa ƙarfi; yakan sha ruwa ya kuma ji gajiya.
13
Kafinta yakan gwada katako yă kuma zāna siffar da alli; yă goge shi da kayan aiki yă kuma zāna shi da alƙalami. Yă siffanta shi a kamannin mutum, mutum cikin dukan darajarsa, don yă ajiye shi a cikin masujada.
14
Yakan ka da itacen saifires, ko kuwa ya ɗauki saifires ko oak. Yă bar shi yă yi girma a cikin itatuwan kurmi, ko yă shuka itacen fir, ruwan sama kuma yă sa yă yi girma.
15
Abin hura wutar mutum ne; yakan ɗebi waɗansu yă hura wuta don yă ji ɗumi, ya hura wuta yă gasa burodi. Amma yakan ƙera zinariya yă kuma yi masa sujada; yakan yi gunki sa’an nan yă rusuna masa.
16
Rabin katakon yakan ƙone a wuta; a kansa yakan dafa abincinsa, yă gasa namansa yă kuma ci sai ya ƙoshi. Yakan ji ɗumi yă kuma ce, “Aha! Na ji ɗumi; na gan wutar.”
17
Da sauran itacen yakan yi allah, gunkinsa; yă rusuna masa yă kuma yi sujada. Yakan yi masa addu’a yă ce, “Ka cece ni; kai ne allahna.”
18
Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba; an rufe idanunsu don kada su gani, tunaninsu kuma a rufe don kada su fahimta.
19
Ba wanda yakan dakata ya yi tunani, ba wanda yake da sani ko fahimi ya ce, “Da rabinsa na yi amfani da shi don hura wuta; na ma gasa burodi a kan garwashinsa, na gasa nama na kuma ci. Ya kamata in yi abin ƙyama daga abin da ya rage? Ya kamata in rusuna wa guntun katako?”
20
Yana cin toka, zuciyar da ta ruɗe tana ɓad da shi; ba zai iya cece kansa ba, ko ya ce, “Wannan abin da yake hannun dama na ba ƙarya ba ne?”
Settings