Ishaya 23:3-18
3
A manyan ruwaye hatsin Shihor suka iso; girbin Nilu ne kuɗin shiga na Taya ta kuma zama kasuwar al’ummai.
4
Ki ji kunya, ya ke Sidon, da ke kuma, kagarar teku, gama teku ya yi magana ya ce, “Ban taɓa naƙuda ba balle in haifi ’ya’ya; ban taɓa goyon ’ya’ya maza ba balle in reno ’ya’ya mata.”
5
Sa’ad da magana ta kai Masar, za su razana da jin labari daga Taya.
6
Ku haye zuwa Tarshish; ku yi kuka mai zafi, ku mutanen tsibiri.
7
Wannan ce birnin murnanku, birnin nan na tun dā wadda ƙafafunta suka kai ta zama a ƙasashe masu nesa?
8
Wane ne ya ƙulla wannan a kan Taya ita da take ba da rawanin sarauta, wadda ’yan kasuwanta sarakuna ne, wadda masu cinikinta sanannu ne a duniya?
9
Ubangiji Maɗaukaki ya ƙulla shi, don yă kawo ƙarshen girman kan dukan darajarta ya kuma ƙasƙantar da dukan waɗanda suke sanannu a duniya.
10
Ki nome ƙasarki har zuwa wajen Nilu, Ya Diyar Tarshish, gama ba ki da tashan jirgin ruwa kuma.
11
Ubangiji ya miƙa hannunsa a bisa teku ya kuma sa mulkokinsa suka yi rawar jiki. Ya ba da umarni game da Funisiya cewa a hallaka kagararta.
12
Ya ce, “Ba za ki ƙara yin murna ba, Ya ke Budurwa Diyar Sidon, yanzu da kike ragargajiya! “Tashi, ki ƙetare zuwa Saifurus; a can ɗin ma ba za ki huta ba.”
13
Dubi ƙasar Babiloniyawa, wannan mutanen da yanzu ba su da wani amfani! Assuriyawa sun mai da ita wurin zaman halittun hamada; sun gina hasumiyoyin kwanto, suka ragargaza kagararta ƙaf suka mai da ita kango.
14
Ku yi kuka mai zafi, ku jiragen ruwan Tarshish; an rurrushe kagararku!
15
A wannan lokaci za a manta da Taya har shekaru saba’in, tsawon rayuwar sarki. Amma a ƙarshen waɗannan shekaru saba’in, zai zama wa Taya kamar yadda yake a waƙar karuwa cewa,
16
“Ɗauki garaya, ki ratsa birni, Ya ke karuwar da aka manta da ita; kaɗa garaya da kyau, ki rera waƙoƙi masu yawa, saboda a tuna da ke.”
17
A ƙarshen shekaru saba’in, Ubangiji zai magance Taya. Za tă koma ga aikinta na karuwanci za tă kuma yi kasuwancinta da dukan mulkokin duniya.
18
Duk da haka za a keɓe ribarta da kuɗin shigarta wa Ubangiji; ba za a yi ajiyarsu ko a ɓoye su. Ribarta za tă tafi ga waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada, don su sami yalwataccen abinci da tufafi masu kyau.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings