Ishaya 23:1-7
1
Abin da Allah ya faɗa game da Taya. Ku yi kuka mai zafi, ya jiragen ruwan Tarshish! Gama an hallaka Taya aka kuma bar su babu gida ko tasha. Daga ƙasar Saifurus magana ta zo musu.
2
Ku yi shiru, ku mutanen tsibiri da ku ’yan kasuwan Sidon waɗanda masu ciniki a teku suka azurta.
3
A manyan ruwaye hatsin Shihor suka iso; girbin Nilu ne kuɗin shiga na Taya ta kuma zama kasuwar al’ummai.
4
Ki ji kunya, ya ke Sidon, da ke kuma, kagarar teku, gama teku ya yi magana ya ce, “Ban taɓa naƙuda ba balle in haifi ’ya’ya; ban taɓa goyon ’ya’ya maza ba balle in reno ’ya’ya mata.”
5
Sa’ad da magana ta kai Masar, za su razana da jin labari daga Taya.
6
Ku haye zuwa Tarshish; ku yi kuka mai zafi, ku mutanen tsibiri.
7
Wannan ce birnin murnanku, birnin nan na tun dā wadda ƙafafunta suka kai ta zama a ƙasashe masu nesa?
Settings