Skip to content
Hosiya 13:1-12

Hosiya 13:1-12

1
Sa’ad da Efraim ya yi magana, mutane sun yi rawan jiki; an girmama shi a cikin Isra’ila. Amma sai ya zama mai laifi na yin wa Ba’al sujada, ya kuwa mutu.
2
Yanzu sai yin zunubi a kai a kai suke; suna yin gumaka wa kansu daga azurfansu, da wayo suna sarrafa siffofi, dukansu aikin masu aikin hannu ne. Ana magana waɗannan mutane cewa, “Suna miƙa hadayar mutum su kuma sumbaci gumakan maruƙa.”
3
Saboda haka za su zama kamar hazon safiya, kamar raɓar safen da yakan kakkaɓe, kamar ƙaiƙayin da ake tankaɗe daga masussuka, kamar hayaƙin da yake fita daga taga.
4
“Amma ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar. Ba za ku yarda da wani Allah ba sai ni, ba wani Mai Ceto in ban da ni.
5
Na lura da ku a hamada, cikin ƙasar mai ƙunar zafi.
6
Sa’ad da na ciyar da su sun ƙoshi; sa’ad da suka ƙoshi, sai suka fara taƙama; sai suka manta da ni.
7
Saboda haka zan hau kansu kamar zaki, zan ɓuya a bakin hanya kamar damisa.
8
Kamar beyar da aka ƙwace mata ’ya’yanta, zan fāɗa musu in ɓarke su. Kamar zaki zan cinye su; kamar naman jeji zan yayyage su.
9
“An hallaka ku, ya Isra’ila, domin kun tayar mini, kun tayar wa mai taimakonku.
10
Ina sarkinku, da zai cece ku? Ina masu mulkinku cikin dukan garuruwanku, waɗanda kuka ce, ‘Ba mu sarki da shugabanni’?
11
Saboda haka cikin fushina na ba ku sarki, kuma cikin hasalata na ɗauke shi.
12
An yi ajiyar laifin Efraim, aka lissafta zunubansa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options