Aller au contenu
Farawa 8:6-19

Farawa 8:6-19

6
Bayan kwana arba’in, sai Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi,
7
ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har sai da ruwa ya shanye a duniya.
8
Sai ya saki kurciya don yă ga in ruwan ya janye daga doron ƙasa.
9
Amma kurciyar ba tă sami inda za tă sa ƙafafunta ba gama akwai ruwa a dukan doron ƙasa, saboda haka ta komo wurin Nuhu a jirgi. Ya miƙa hannunsa ya ɗauko kurciyar ya shigar da ita wurinsa a cikin jirgi.
10
Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar daga jirgi.
11
Sa’ad da kurciya ta komo wurinsa da yamma, sai ga ɗanyen ganyen zaitun da ta tsinko a bakinta! Sa’an nan Nuhu ya san cewa ruwa ya janye daga duniya.
12
Ya ƙara jira kwana bakwai, sai ya sāke aiken kurciyar, amma a wannan ƙaro ba tă komo wurinsa ba.
13
A rana ta fari ga wata na fari wanda Nuhu ya cika shekaru 601, ruwa ya shanye a ƙasa. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya ga cewa doron ƙasa ya bushe.
14
A ran ashirin da bakwai ga wata na biyu, ƙasa ta bushe ƙaƙaf.
15
Sa’an nan Allah ya ce wa Nuhu,
16
“Fito daga jirgin, kai da matarka da ’ya’yanka maza da matansu.
17
Ka fitar da kowane iri halitta mai rai da take tare da kai waje, tsuntsaye, dabbobi, da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa, don su yi ta haihuwa, su yi yawa, su ƙaru a duniya.”
18
Sai Nuhu ya fito tare da matarsa da ’ya’yansa maza da matan ’ya’yansa,
19
da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abu da yake tafiya a bisa duniya, suka fito daga jirgi daki-daki bisa ga irinsu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options