Skip to content
Farawa 37:1-9

Farawa 37:1-9

1
Yaƙub ya zauna a ƙasar da mahaifinsa ya zauna, wato, ƙasar Kan’ana.
2
Wannan shi ne labarin zuriyar Yaƙub. Yusuf, saurayi ne mai shekara goma sha bakwai. Shi da ’yan’uwansa, wato, ’ya’yan Bilha maza da kuma ’ya’yan Zilfa maza, matan mahaifinsa suna kiwon garkuna tare. Sai Yusuf ya kawo wa mahaifinsu rahoto marar kyau game da ’yan’uwansa.
3
Isra’ila dai ya fi ƙaunar Yusuf fiye da kowanne a cikin sauran ’ya’yansa maza, gama an haifa masa shi a cikin tsufansa. Sai ya yi masa riga mai gwanin kyau.
4
Sa’ad da ’yan’uwansa suka ga cewa mahaifinsu ya fi ƙaunarsa fiye da kowanne daga cikinsu, sai suka ƙi jininsa, ba sa kuma maganar alheri da shi.
5
Sai Yusuf ya yi mafarki, sa’ad da ya faɗa wa ’yan’uwansa, suka ƙara ƙin jininsa.
6
Ya ce musu, “Ku saurari wannan mafarkin da na yi.
7
Muna daurin dammunan hatsi a gona, sai nan da nan damina ya tashi ya tsaya, yayinda dammunanku suka taru kewaye da nawa suka rusuna masa.”
8
Sai ’yan’uwansa suka ce masa, “Kana nufin za ka yi mulki a kanmu ke nan? Ko kuwa za ka zama sarki, a bisanmu?” Suka ƙara ƙin jininsa saboda mafarkinsa da kuma abin da ya faɗa.
9
Sai Yusuf ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa ’yan’uwansa. Ya ce, “Ku saurara, na sāke yin wani mafarki, a wannan lokaci, na ga rana da wata da taurari goma sha ɗaya suna rusuna mini.”

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options