Farawa 36:1-8
1
Waɗannan su ne zuriyar Isuwa (wato, Edom).
2
Isuwa ya ɗauko matansa daga cikin matan Kan’ana, ya ɗauko Ada ’yar Elon mutumin Hitti, da Oholibama ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon Bahiwiye
3
ya kuma auri Basemat ’yar Ishmayel wadda take ’yar’uwar Nebayiwot.
4
Ada ta haifi wa Isuwa, Elifaz. Basemat kuma ta haifa masa Reyuwel.
5
Oholibama kuwa ta haifa masa Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza, waɗanda aka haifa masa a Kan’ana.
6
Isuwa ya ɗauki matansa da ’ya’yansa maza da mata da kuma dukan membobin gidansa, ya kuma ɗauki shanunsa da dukan sauran dabbobinsa, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan’ana zuwa wata ƙasa nesa da ɗan’uwansa Yaƙub.
7
Mallakarsu ta yi yawa ƙwarai da ba za su iya zauna tare ba; gama ƙasar da suke zaune a ciki ba za tă ishe su su biyu ba saboda dabbobinsu.
8
Saboda haka Isuwa (wato, Edom) ya zauna a ƙasar tuddai na Seyir.
Settings