Farawa 34:15-24
15
Za mu yarda da wannan kaɗai ta wannan sharaɗi, cewa za ku zama kamar mu ta wurin yin wa dukan ’ya’yanku maza kaciya.
16
Sa’an nan za mu ba da ’ya’yanmu mata aure gare ku, mu kuma mu aure ’ya’yanku mata wa kanmu. Za mu zauna a cikinku mu kuma zama mutane ɗaya da ku.
17
Amma in ba za ku yarda a yi muku kaciya ba, za mu ɗauki ’yar’uwanmu mu tafi.”
18
Sharuɗansu sun gamshi Hamor da ɗansa, Shekem.
19
Saurayin wanda aka fi girmamawa a cikin dukan gidan mahaifinsa, bai ɓata lokaci a yin abin da suka ce ba, domin ya ji daɗin ’yar Yaƙub.
20
Saboda haka Hamor da ɗansa Shekem suka tafi ƙofar birninsu don su yi magana da mutanen garinsu.
21
Suka ce, “Waɗannan mutane ba su da damuwa, bari su zauna a cikin ƙasarmu, su kuma yi sana’a a ciki; ƙasar tana da isashen fili dominsu. Za mu iya auro ’ya’yansu mata, su kuma su auri namu.
22
Amma mutanen za su yarda su zauna tare da mu kamar mutane ɗaya kawai bisa wannan sharaɗi, cewa a yi wa mazanmu kaciya, kamar yadda su kansu suke.
23
Ashe, shanunsu, dukiyarsu da dukan sauran dabbobinsu, ba za su zama namu ba? Saboda haka mu yarda, za su kuwa zauna a cikinmu.”
24
Dukan mazan da suka fito ƙofar birnin suka yarda da Hamor da kuma ɗansa Shekem, aka kuwa yi wa kowane namiji a birnin kaciya.
Settings