Farawa 34:13-17
13
Domin an ɓata ’yar’uwansu Dina, sai ’ya’yan Yaƙub maza suka amsa a ha’ince yayinda suke wa Shekem da mahaifinsa Hamor magana.
14
Suka ce musu, “Ba za mu iya yin wannan abu ba, ba za mu iya ba da ’yar’uwarmu ga mutumin da ba shi da kaciya ba. Wannan zai zama abin kunya ne a gare mu.
15
Za mu yarda da wannan kaɗai ta wannan sharaɗi, cewa za ku zama kamar mu ta wurin yin wa dukan ’ya’yanku maza kaciya.
16
Sa’an nan za mu ba da ’ya’yanmu mata aure gare ku, mu kuma mu aure ’ya’yanku mata wa kanmu. Za mu zauna a cikinku mu kuma zama mutane ɗaya da ku.
17
Amma in ba za ku yarda a yi muku kaciya ba, za mu ɗauki ’yar’uwanmu mu tafi.”
Settings