Skip to content
Farawa 24:46-61

Farawa 24:46-61

46
“Ta yi sauri ta saukar da tulun daga kafaɗarta ta ce, ‘Sha, zan kuma ba wa raƙumanka su ma.’ Sai na sha, ta kuma shayar da raƙumana su ma.
47
“Na tambaye ta, ‘Ke ’yar wane ne?’ “Ta ce, ‘’Yar Betuwel ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa.’ “Sai na sa mata zobe a hancinta, woroworo kuma a hannuwata,
48
na kuma sunkuya na yi wa Ubangiji sujada. Na yabi Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim wanda ya bi da ni a hanyar da take daidai, don in samo wa ɗan maigidana jikanyar ɗan’uwansa.
49
Yanzu fa in za ku nuna wa maigidana alheri da aminci, ku faɗa mini, in kuma ba haka ba, ku faɗa mini, don in san hanyar da zan juya.”
50
Laban da Betuwel suka ce, “Wannan daga wurin Ubangiji ne, ba abin da za mu ce I, ko a’a ba.
51
Ga Rebeka, ɗauke ta ku tafi, bari tă zama matar ɗan maigidanka, yadda Ubangiji ya umarta.”
52
Sa’ad da bawan Ibrahim ya ji abin da suka ce, sai ya rusuna har ƙasa a gaban Ubangiji.
53
Sa’an nan bawan ya fito da kayan ado na zinariya da azurfa da kayayyaki na tufafi ya ba wa Rebeka; ya kuma ba wa ɗan’uwanta da mahaifiyarta kyautai masu tsada.
54
Sa’an nan shi da mutanen da suke tare da shi suka ci, suka sha, suka kuma kwana a can. Kashegari da safe da suka tashi sai ya ce, “A sallame ni in koma wurin maigidana.”
55
Amma ɗan’uwanta da mahaifiyarta suka ce, “Bari yarinyar ta ɗan zauna tare da mu kwana goma ko fiye, sa’an nan ka ta fi.”
56
Amma ya ce musu, “Kada ku tsai da ni, tun da Ubangiji ya ba ni nasara a tafiyata. Ku sallame ni domin in tafi wurin maigidana.”
57
Sa’an nan suka ce, “Bari mu kira yarinyar mu tambaye ta game da zancen.”
58
Saboda haka suka kira Rebeka suka ce mata, “Za ki tafi tare da mutumin nan?” Sai ta ce, “Zan tafi.”
59
Saboda haka suka sallame Rebeka, ’yar’uwarsu, duk da uwar goyonta da bawan Ibrahim da mutanensa.
60
Suka kuma albarkaci Rebeka suka ce mata, “’Yar’uwarmu, bari ki zama mahaifiyar dubu dubbai, bari zuriyarki su mallaki ƙofofin abokan gābansu.”
61
Sa’an nan Rebeka da bayinta mata suka shirya suka hau raƙumansu suka koma tare da mutumin. Da haka bawan ya ɗauki Rebeka ya tafi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options