Skip to content
Farawa 24:1-15

Farawa 24:1-15

1
Yanzu fa Ibrahim ya tsufa, yana da shekaru masu yawa, Ubangiji kuma ya albarkace shi a kowace hanya.
2
Sai Ibrahim ya ce wa babban bawan gidansa, wanda yake lura da duk abin da yake da shi, “Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata.
3
Ina so ka rantse da sunan Ubangiji Allah na sama da ƙasa, cewa ba za ka samo wa ɗana mata daga ’yan matan Kan’aniyawa, waɗanda nake zama cikinsu ba.
4
Amma za ka tafi ƙasata da kuma cikin ’yan’uwana, ka samo mata saboda ɗana Ishaku.”
5
Bawan ya ce masa, “Me zai faru in matar ba tă yarda tă zo tare da ni zuwa wannan ƙasa ba? In komar da ɗanka a ƙasar da ka fito ne ke nan?”
6
Ibrahim ya ce, “Ka tabbata ba ka komar da ɗana can ba.”
7
Ubangiji Allah na sama, wanda ya fitar da ni daga gidan mahaifina, da kuma ƙasar asalina wanda kuma ya yi magana da ni, ya yi mini alkawari da rantsuwa cewa, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa, zai aika mala’ikansa yă sha gabanka domin ka samo wa ɗana mata daga can.
8
In matar ba tă yarda tă zo tare da kai ba, za a kuɓutar da kai daga wannan rantsuwa. Sai dai kada ka kai ɗana a can.”
9
Saboda haka bawan ya sa hannunsa a ƙarƙashin cinyar maigidansa Ibrahim, ya kuma rantse masa game da wannan al’amari.
10
Sai bawan ya ɗibi raƙuma goma na maigidansa ya tafi, ɗauke da kowane irin abubuwa masu kyau daga wurin maigidansa. Ya fita don yă tafi Aram-Naharayim, ya kama hanyarsa zuwa garin Nahor.
11
Ya sa raƙuman suka durƙusa kusa da rijiya a bayan gari; wajen yamma ne, lokacin da mata sukan fita ɗiban ruwa.
12
Sai ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, ka ba ni nasara yau, ka kuma nuna alheri ga maigidana Ibrahim.
13
Duba, ina tsaye a bakin rijiyar ruwa, ’ya’ya matan mutanen gari kuma suna fitowa domin ɗiban ruwa.
14
Bari yă zama sa’ad da na ce wa wata yarinya, ‘Ina roƙonki ki saukar da tulunki domin in sha,’ in ta ce, ‘Ka sha, zan kuma ba wa raƙumanka ma’; bari tă zama ita ce ka zaɓa wa bawanka Ishaku. Ta haka zan san cewa ka nuna wa maigidana alheri.”
15
Kafin ya gama addu’a, sai Rebeka ta fito da tulu a kafaɗarta. Ita ’yar Betuwel ɗan Milka, matar Nahor, ɗan’uwan Ibrahim.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options