Skip to content
Farawa 21:9-21

Farawa 21:9-21

9
Amma Saratu ta ga cewa yaron da Hagar, mutuniyar Masar ta haifa wa Ibrahim yana wa ɗanta Ishaku gori,
10
sai ta ce wa Ibrahim, “Ka kori baiwan nan tare da ɗanta, saboda ɗan baiwan nan ba zai taɓa raba gādo da ɗana Ishaku ba.”
11
Al’amarin ya ɓata wa Ibrahim rai sosai domin zancen ya shafi ɗansa.
12
Amma Allah ya ce wa Ibrahim, “Kada hankalinka yă tashi game da yaron nan da kuma baiwarka. Ka saurari duk abin da Saratu ta faɗa maka, saboda ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.
13
Zan ba ɗan baiwan nan al’umma shi ma, domin shi zuriyarka ne.”
14
Kashegari da sassafe sai Ibrahim ya ɗauki abinci da salkar ruwa, ya ba wa Hagar. Ya ɗora su a kafaɗunta, sa’an nan ya sallame ta da yaron. Ta kama hanyarta ta kuma yi ta yawo a cikin jejin Beyersheba.
15
Sa’ad da ruwan da yake cikin salkan ya ƙare, sai ta ajiye yaron a ƙarƙashin wani ƙaramin itace.
16
Sai ta tafi, ta zauna ɗan nesa da yaron, misalin nisan harbin baka, gama ta yi tunani ta ce, “Ba zan iya kallon yaron yana mutuwa ba.” Da ta zauna nesa da yaron, sai ta fara kuka.
17
Allah kuwa ya ji yaron yana kuka, sai mala’ikan Allah ya kira Hagar daga sama ya ce mata, “Mene ne damuwarki, Hagar? Kada ki ji tsoro, Allah ya ji yaron yana kuka yayinda yake kwance a can.
18
Ki ɗaga yaron ki riƙe shi a hannu, gama zan mai da shi al’umma mai girma.”
19
Sa’an nan Allah ya buɗe idanunta ta ga wata rijiyar ruwa. Don haka sai ta tafi ta cika salkan da ruwa, ta kuma ba wa yaron ruwa ya sha.
20
Allah ya kasance da yaron, yayinda yake girma. Ya yi zama a jeji, ya kuma zama maharbi.
21
Yayinda yake zama a Jejin Faran, sai mahaifiyarsa ta samo masa mata daga Masar.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options