Farawa 21:22-34
22
A lokacin nan Abimelek da Fikol, komandan rundunoninsa suka zo suka ce wa Ibrahim, “Allah yana tare da kai a ko mene ne kake yi.
23
Yanzu ka rantse mini a nan a gaban Allah cewa, ba za ka yaudare ni ko ’ya’yana ko kuma zuriyata ba. Ka nuna mini alheri, kai da ƙasar da kake zama baƙunci kamar yadda na nuna maka.”
24
Ibrahim ya ce, “Na rantse.”
25
Sa’an nan Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek game da rijiyar ruwan da bayin Abimelek suka ƙwace.
26
Sai Abimelek ya ce, “Ban san wanda ya yi wannan ba. Ba ka faɗa mini ba, ban kuwa taɓa ji ba, sai yau.”
27
Sai Ibrahim ya kawo tumaki da shanu ya ba wa Abimelek, sai su biyun suka yi yarjejjeniya.
28
Ibrahim ya ware ’yan raguna bakwai daga cikin garke,
29
sai Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Mene ne ma’anar ’yan raguna bakwai da ka keɓe?”
30
Ibrahim ya amsa ya ce, “Ka karɓi waɗannan ’yan tumaki bakwai daga hannuna a matsayin shaida cewa ni ne na haƙa wannan rijiya.”
31
Saboda haka aka kira wurin Beyersheba, domin a nan ne su biyun suka yi rantsuwa.
32
Bayan da aka yi yarjejjeniya a Beyersheba, sai Abimelek da Fikol, komandan rundunoninsa suka koma ƙasar Filistiyawa.
33
Sai Ibrahim ya shuka itacen tsamiya a Beyersheba, a can kuma ya kira bisa sunan Ubangiji, Allah Madawwami.
34
Ibrahim kuwa ya zauna a ƙasar Filistiyawa na dogon lokaci.
Settings