Farawa 14:17-24
17
Bayan Abram ya dawo daga cin Kedorlayomer da sarakunan da suka haɗa kai da shi a yaƙi, sai sarkin Sodom ya fito don yă tarye Abram a Kwarin Shabe (wato, Kwarin Sarki).
18
Sai Melkizedek sarkin Salem ya kawo burodi da ruwan inabi. Shi firist ne na Allah Mafi Ɗaukaka,
19
ya albarkaci Abram yana cewa, “Allah Mafi Ɗaukaka Mahaliccin sama da ƙasa yă albarkace Abram.
20
Kuma albarka ta tabbata ga Allah Mafi Ɗaukaka wanda ya ba da maƙiyanka a hannunka.” Sa’an nan Abram ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na kome.
21
Sarkin Sodom ya ce wa Abram, “Ka ba ni mutanena da ka ƙwace daga hannun sarakunan nan kawai, ka riƙe kayayyakin don kanka.”
22
Amma Abram ya ce, wa sarkin Sodom, “Na ɗaga hannu ga Ubangiji Allah Mafi Ɗaukaka, Mahaliccin sama da ƙasa, na riga na rantse
23
cewa ba zan karɓi kome da yake naka ba, ko zare ko maɗaurin takalma, don kada ka ce, ‘Na azurta Abram.’
24
Ba zan karɓi kome ba, sai dai abin da mutanena suka ci da kuma rabon mutanen da suka tafi tare da ni, ga Aner, Eshkol, da Mamre. Bari su ɗauki rabonsu.”
Settings