Farawa 14:13-16
13
Sai wani wanda ya tsira, ya zo ya faɗa wa Abram mutumin Ibraniyawa. Abram kuwa yana zama kusa da manyan itatuwan Mamre, Mamre mutumin Amoriyawa ne ɗan’uwan Eshkol da Aner, su kuwa abokan Abram ne.
14
Da Abram ya ji cewa an kama danginsa, sai ya tara horarrun mutane 318, da aka haifa a gidansa, ya bi sawun sarakunan da suka tafi da Lot, har Dan.
15
Da dad dare, Abram ya rarraba mutanensa don su fāɗa wa sarakunan nan, ya ɗibge su, ya kore su har zuwa Hoba, arewa da Damaskus.
16
Ya washe su da kuma dukan kayayyakinsu, ya kuma dawo da Lot danginsa da mallakarsa, tare da mata da sauran mutane.
Settings