Skip to content
Galatiyawa 2:1-10

Galatiyawa 2:1-10

1
Bayan shekara goma sha huɗu sai na sāke haurawa zuwa Urushalima, a wannan lokaci na tafi tare da Barnabas. Na kuma ɗauki Titus muka tafi tare.
2
Na tafi ne bisa ga wani wahayi. Da na kai can, sai na bayyana musu bisharar da nake wa’azi a cikin Al’ummai. Na yi haka a keɓance a gaban waɗanda suke shugabanni, don tsoro kada gudun da nake yi, ko kuwa na riga na yi, yă zama a banza.
3
Amma ko Titus ma da yake tare da ni, ba a ce dole sai ya yi kaciya ba, ko da yake shi mutumin Al’ummai ne.
4
Wannan zancen kaciya ya taso domin waɗansu ’yan’uwan ƙarya sun shiga cikinmu domin su yi leƙe a kan ’yancin da muke da shi a cikin Kiristi Yesu, su kuma mai da mu bayi.
5
Ba mu kuwa ba su zarafi ba ko kaɗan, don gaskiyar bishara ta ci gaba da kasance tare da ku.
6
Game da waɗanda aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne, ko wane ne su, duk ɗaya ne a wurina; gama Allah ba ya nuna bambanci, ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙara mini kome ba.
7
A maimakon haka, sun ga cewa an danƙa mini hakkin wa’azin bishara ga Al’ummai, kamar yadda aka danƙa wa Bitrus ga Yahudawa.
8
Gama Allah wanda ya yi aiki a cikin hidimar Bitrus a matsayin manzo ga Yahudawa, haka ma ya yi aiki a cikin hidimata a matsayin manzo ga Al’ummai.
9
Yaƙub, Bitrus da Yohanna waɗanda suke fitattun ginshiƙai, sun karɓe ni da Barnabas da hannu biyu biyu sa’ad da suka gane alherin da aka ba ni. Suka kuma yarda cewa ya kamata mu tafi wajen Al’ummai, su kuwa su tafi wajen Yahudawa.
10
Abin da dai suka roƙa shi ne ya kamata mu riƙa tuna da matalauta, abin nan da nake marmarin yi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options