Ezra 5:2-12
2
Sa’an nan Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da Yeshuwa ɗan Yozadak suka yi shiri suka kama aikin sāke gina gidan Allah a Urushalima. Annabawan Allah kuwa suna tare da su, suna taimakonsu.
3
A wannan lokaci, Tattenai gwamnan Kewayen Kogin Yuferites, da Shetar-Bozenai da abokansu suka je wurinsu suka tambaye su cewa, “Wa ya ba ku iko ku sāke gina wannan haikali har ku gyara katangar?”
4
Suka kuma tambaye su “Ina sunayen waɗanda suke wannan gini?”
5
Amma Allah yana tsaron dattawan Yahudawa, saboda haka ba a hana su aikin ba har sai rahoto ya kai wurin Dariyus aka kuma sami amsarsa a rubuce tukuna.
6
Ga wasiƙar da Tattenai, gwamnan Kewayen Kogin Yuferites, da Shetar-Bozenai da abokansu masu riƙe da muƙamai a Kewayen Kogin Yuferites suka aika wa Sarki Dariyus.
7
Ga rahoton da suka aika masa. Zuwa ga Sarki Dariyus. Gaisuwa da fatan alheri.
8
Ya kamata sarki yă sani cewa mun je yankin Yahuda, zuwa gidan Allah mai girma. Muka ga mutanen suna ginin haikalin da manyan duwatsu, suna sa katakai a bangon. Ana aikin da ƙwazo, aikin kuma yana cin gaba sosai, suna kuma lura da shi.
9
Mun tambayi dattawan muka ce musu, “Wa ya ba ku iko ku sāke gina wannan haikali, ku kuma sāke gyara katangarsa?”
10
Muka kuma tambaye su sunayensu don mu rubuta mu sanar da kai waɗanda suke shugabanninsu.
11
Wannan ita ce amsar da suka ba mu. “Mu bayin Allah na sama da ƙasa ne, muna sāke gina haikalin da aka gina tun shekaru da yawa da suka wuce, da wani babban sarkin Isra’ila ya gina ya kuma gama.
12
Amma domin kakanninmu sun ɓata wa Allah na sama rai, sai ya bari suka fāɗa cikin hannun Nebukadnezzar mutumin Kaldiya, sarkin Babilon, wanda ya rushe wannan haikali, ya kuma kwashe mutane zuwa Babilon.
Settings