Ezekiyel 16:1-14
1
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
2
“Ɗan mutum, ka sa Urushalima ta san ayyukanta masu banƙyama
3
ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wa Urushalima, Asalinki da haihuwarki daga ƙasar Kan’ana ne; mahaifinki mutumin Amoriyawa ne, mahaifiyarki kuma mutuniyar Hitti ce.
4
A ranar da aka haife ki ba a yanke cibiyarki ba, ba a kuma yi miki wanka don a tsabtacce ki ba, ba a kuma goge ki da gishiri ba ko a naɗe ki cikin tsummoki.
5
Ba wanda ya dube ki da tausayi ko ya nuna miki isashen jinƙai don yă yi miki ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa. A maimako, sai aka jefar da ke a fili, gama a ranar da aka haife ki an ji ƙyamarki.
6
“ ‘Sa’an nan na wuce na ga kina birgima cikin jininki, yayinda kike kwance can cikin jininki sai na ce miki, “Ki rayu!”
7
Na sa kin yi girma kamar tsiro a fili. Kin yi girma kika kuma yi tsayi kika zama mafiya kyau na kayan ado. Nononki suka fito, gashinki kuwa suka yi girma, duk da haka tsirara kike tik.
8
“ ‘Daga baya na wuce, da na dube ki sai na ga cewa kin yi girma sosai har kin kai a ƙaunace ki, na yafa gefen tufafina a kanki na kuma rufe tsiraincinki. Na rantse miki, na ƙulla alkawari da ke, kin kuwa zama tawa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
9
“ ‘Na yi miki wanka na wanke miki jini daga gare ki na kuma shafa miki mai.
10
Na rufe ki da rigar da aka yi wa ado na kuma sa miki takalman fata. Na sa miki riga ta lilin mai kyau na kuma rufe ki da riguna masu tsada.
11
Na yi miki ado da kayan ado masu daraja, na sa miki mundaye a hannuwanki da abin wuya a wuyanki,
12
na kuma sa miki zobe a hancinki, abin kunne a kunnuwanki da rawani mai kyau a kanki.
13
Haka kuwa aka caɓa miki zinariya da azurfa; tufafinki kuwa na lilin mai kyau da riguna masu tsada waɗanda aka yi musu ado. Abincinki na gari mai laushi ne, zuma da man zaitun. Kika zama kyakkyawa har kika kuma zama sarauniya.
14
Sunanki ya yaɗu a cikin al’ummai saboda kyanki, domin darajar da na ba ki ya sa kyanki ya zama cikakke, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Settings