Ezekiyel 16:15-34
15
“ ‘Amma kika dogara ga kyanki kika kuma yi amfani da sunan da kika yi don ki zama karuwa. Kin yi ta jibga alherai a kan kowa da ya wuce, sai kyanki ya zama naki.
16
Kin ɗauki waɗansu tufafinki don ki yi wa kanki masujadai masu ado, inda kike karuwancinki. Irin waɗannan abubuwa bai kamata su faru ba, bai kuma kamata su taɓa faruwa ba.
17
Kika kuma ɗauki kayan ado masu kyau da na ba ki, kayan adon da aka yi da zinariya da azurfa, kika yi wa kanki gumakan maza kika kuma yi ta yin karuwanci da su.
18
Kika ɗauki rigunanki masu ado don ki sa a kansu, kika kuma miƙa maina da turarena a gabansu.
19
Haka ma abincin da na tanada miki, lallausan gari, man zaitun, da zuman da na ba ki ki ci, kin miƙa su kamar turare mai ƙanshi a gabansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
20
“ ‘Kika kuma kwashe ’ya’yanki maza da mata waɗanda kin haifa mini kika miƙa su kamar abinci ga gumakanki. Karuwancinki bai isa ba ne?
21
Kin kashe ’ya’yana kika kuma miƙa su ga gumaka.
22
Cikin dukan ayyukan banƙyamarki da karuwancinki ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba, sa’ad da kike tsirara tik, kina birgima cikin jininki.
23
“ ‘Kaito! Kaitonki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Bugu da ƙari a kan dukan waɗansu muguntarki,
24
kin gina wa kanki ɗakunan sama da gidajen tsafi a kowane dandali.
25
A kowane titi kin gina ɗakin tsafi kika kuma wulaƙanta kyanki, kina miƙa jikinki da ƙarin fasikanci ga duk mai wucewa.
26
Kin yi karuwanci da Masarawa, maƙwabtanki masu kwaɗayi, kika tsokane ni har na yi fushi da ƙarin fasikancinki.
27
Saboda haka na miƙa hannuna gāba da ke na kuma rage iyakarki; na ba da ke ga abokan gābanki masu haɗama, ’yan matan Filistiyawa, waɗanda suka sha mamaki saboda halinki na lalata.
28
Kin kuma yi karuwanci da Assuriyawa, domin ba kya ƙoshi; kai ko bayan wannan, ba ki ƙoshi ba.
29
Sai kika ƙara fasikancinki da ya haɗa da ƙasar cinikin Babilon, amma duk da haka ba ki ƙoshi ba.
30
“ ‘Kina da rashin ƙarfi a zuci, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, sa’ad da kika yi duk waɗannan abubuwa, kina yi kamar karuwar da aka watsa!
31
Sa’ad da kika gina ɗakunan samanki a kowane gefen titi kika kuma gina ɗakunan tsafinki a kowane dandali, ba kamar karuwa kike ba, domin kin karɓi kuɗi.
32
“ ‘Ke mazinaciyar mace! Kin gwammace baƙi a maimakon mijinki!
33
Kowace karuwa kan karɓi kuɗi, amma kina ba da kyautai ga dukan kwartayenki, kina ba su cin hanci don su zo wurinki daga ko’ina don alherai marasa ƙa’ida.
34
Saboda haka cikin karuwancinki kin sha bamban da saura; babu wanda yake binki saboda alheranki. Ke dai dabam ce, gama kikan biya kuma ba mai biyanki.
Settings