Skip to content
Fitowa 40:16-33

Fitowa 40:16-33

16
Musa ya aikata dukan kome yadda Ubangiji ya umarce shi.
17
Da haka aka kafa tabanakul, a rana ta fari ga wata na fari a shekara ta biyu.
18
Sa’ad da Musa ya kafa tabanakul, ya sa rammuka a wurinsu, ya sa katakan, ya kuma sa sandunan, ya kakkafa dogayen sandunan.
19
Sa’an nan ya shimfiɗa tentin a bisa tabanakul, ya kuma sa murfi a bisa tentin, yadda Ubangiji ya umarce shi.
20
Ya ɗauki dokokin Alkawari ya sa a cikin akwatin, ya kuma zura sandunan a zoban akwatin, sa’an nan ya sa murfin kafara a bisansa.
21
Sai ya kawo akwatin a cikin tabanakul, ya kuma rataye labulen rufewa ya tsare akwatin Alkawarin, yadda Ubangiji ya umarce shi.
22
Musa ya sa teburin a Tentin Sujada, a gefen arewa na tabanakul waje da labulen.
23
Ya shirya burodin a kai a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.
24
Ya sa wurin ajiye fitilan a Tentin Sujada ɗaura da teburin a gefen kudu na tabanakul
25
ya kuma shirya fitilun a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.
26
Musa ya sa bagaden zinariya a cikin Tentin Sujada a gaban labulen
27
ya ƙone turare mai ƙanshi a kai, yadda Ubangiji ya umarce shi.
28
Sa’an nan ya sa labule a ƙofar shiga na tabanakul.
29
Ya sa bagaden hadaya ta ƙonawa kusa da ƙofar tabanakul, Tentin Sujada, sa’an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari a kansa, yadda Ubangiji ya umarce shi.
30
Ya sa daro tsakanin Tentin Sujada da bagade, ya kuma zuba ruwa a cikinsa don wanki,
31
a cikin kuwa Musa da Haruna da ’ya’yansa maza sukan wanke hannunsa da ƙafafunsu.
32
Sukan yi wanka a duk sa’ad da suka shiga Tentin Sujada, ko in suka kusaci bagade, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
33
Sa’an nan Musa ya yi fili kewaye da tabanakul da kuma bagaden, ya rataye labule a ƙofar shiga filin. Da haka Musa ya gama aikin.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options