Skip to content
Fitowa 40:1-15

Fitowa 40:1-15

1
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,
2
“Ka kafa tabanakul, da Tentin Sujada, a kan rana ta fari ga watan fari.
3
Ka sa akwatin Alkawari a cikinsa, sa’an nan ka rufe shi da labule.
4
Ka shigar da teburin ka shirya kayayyakin a kansa. Sa’an nan ka shigar da wurin ajiye fitilan ka kuma sa fitilunsa.
5
Ka sa bagaden zinariya na ƙona turare a gaban akwatin Alkawari, ka kuma sa labule a ƙofar shiga tabanakul.
6
“Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar tabanakul, da Tentin Sujada;
7
ka ajiye daron tsakanin Tentin Sujada da bagaden, ka kuma zuba ruwa a cikinsa.
8
Ka yi fili kewaye da shi, ka kuma sa labule a ƙofar shiga filin.
9
“Ka ɗauki man shafewa ka shafe tabanakul da duka abin da yake cikinsa; ka keɓe shi da dukan kayayyakinsa, zai zama tsarkake.
10
Sa’an nan ka shafe bagaden hadaya ta ƙonawa da kayansa; ka keɓe bagaden, zai zama mai tsarki.
11
Ka shafe daron da wurin ajiyarsa, ka kuma keɓe su.
12
“Ka kawo Haruna da ’ya’yansa a ƙofar Tentin Sujada ka wanke su da ruwa.
13
Sa’an nan ka sa wa Haruna tsarkakun riguna, ka shafe shi, ka kuma keɓe shi don yă yi mini hidima a matsayin firist.
14
Ka kawo ’ya’yansa maza ka sa musu taguwoyi.
15
Ka shafe su yadda ka shafe mahaifinsu, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Shafe musu man, zai sa su zama firistoci na ɗinɗinɗin, dukan zamanansu.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options