Fitowa 16:1-15
1
Dukan taron Isra’ila suka tashi daga Elim suka zo hamadar Sin, wadda take tsakanin Elim da Sinai, a rana ta goma sha biyar ga wata biyu, bayan sun fito daga Masar.
2
A hamadan, dukan taro suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna.
3
Isra’ilawa suka ce musu, “Da ma a hannun Ubangiji ne muka mutu a Masar, inda muka zauna kewaye da tukwanen nama, muna cin duk abincin da muke so, amma kun kawo mu cikin wannan hamada don ku kashe dukan wannan taro da yunwa.”
4
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan zubo muku burodi kamar ruwa daga sama. Mutanen za su fita kowace rana su tattara abin da zai ishe su na ranan. Ta haka zan gwada su in ga ko za su bi umarnaina.
5
A rana ta shida za su shirya abin da suka kwaso, wannan kuwa zai zama ninki biyu na abin da sukan tattara na sauran ranaku.”
6
Saboda haka Musa da Haruna suka ce wa dukan Isra’ila, “Da yamma za ku sani Ubangiji ne ya fitar da ku daga Masar.
7
Da safe za ku ga ɗaukakar Ubangiji, saboda ya ji gunaguninku a kansa. Wane mu, da za ku yi gunaguni a kanmu?”
8
Musa ya kuma ce, “Za ku san cewa shi ne Ubangiji, sa’ad da ya ba ku nama ku ci da yamma, da kuma duk burodin da kuke so da safe, saboda ya ji gunagunin da kuka yi a kansa. Namu a wane? Ai, gunaguninku ba a kanmu ba, amma a kan Ubangiji ne.”
9
Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ka faɗa wa dukan taron Isra’ila, ‘Ku zo gaban Ubangiji, gama ya ji gunaguninku.’ ”
10
Yayinda Haruna yake magana da dukan taron Isra’ila, sai suka duba wajen hamada, sai ga ɗaukakar Ubangiji tana bayyana a girgije.
11
Ubangiji ya ce wa Musa,
12
“Na ji gunagunin Isra’ilawa. Ka faɗa musu, ‘A tsakanin fāɗuwar rana da almuru, za ku ci nama, da safe kuma za ku ƙoshi da burodi. Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”
13
Da yamman wannan rana, sai makware suka rufe dukan sansani, da safe kuma sai ga raɓa ta kewaye sansani.
14
Lokacin da raɓar ta watse, sai ga wani abu kamar tsaki, falle-falle kuma da laushi, fari, kamar hazo, a ƙasa.
15
Sa’ad da Isra’ilawa suka ga wannan, sai suka ce wa junansu, “Mene ne wannan?” Gama ba su san ko mene ne ba. Musa ya ce musu, “Wannan shi ne burodin da Ubangiji ya ba ku ku ci.
Settings