Fitowa 16:22-30
22
A rana ta shida, suka tattara ninki biyu, mudu biyu ga mutum guda, sai shugabannin taron suka zo suka kawo ƙara wurin Musa.
23
Shi kuma ya ce musu, “Wannan shi ne umarnin Ubangiji, ‘Gobe za tă zama ranar hutu, Asabbaci mai tsarki ga Ubangiji. Domin haka sai ku toya abin da kuke so ku toya, ku kuma dafa abin da kuke so ku dafa. Abin da ya rage ku ajiye har safe.’ ”
24
Sai suka bar saura har safe, kamar yadda Musa ya umarta, bai kuwa yi wari ko yă yi tsutsa ba.
25
Musa ya ce, “Ku ci shi yau, saboda yau Asabbaci ne na Ubangiji. Ba za ku same shi a ƙasa a yau ba.
26
Kwana shida za ku tattara shi, amma a rana ta bakwai, Asabbaci, ba za a same shi ba.”
27
Duk da haka waɗansu mutane suka fita a ranar Asabbaci don su tattara, amma ba su sami kome ba.
28
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe za ku ƙi bin dokokina da umarnaina?
29
Ku lura fa, ai, Ubangiji ne ya ba ku Asabbaci; shi ya sa a kan ba ku burodi na kwana biyu, a rana ta shida. Kowa ya kamata yă kasance inda yake a rana ta bakwai; kada kowa yă fita.”
30
Sai mutanen suka huta a rana ta bakwai.
Settings