Skip to content
Fitowa 10:1-11

Fitowa 10:1-11

1
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je wurin Fir’auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da kuma zukatan fadawansa domin in aikata waɗannan mu’ujizai nawa a tsakiyarsu,
2
don kuma ku gaya wa ’ya’yanku da jikokinku yadda na tsananta wa Masarawa, da kuma yadda na aikata mu’ujizai a cikinsu, don ku sani ni ne Ubangiji.”
3
Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce masa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Ibraniyawa ya ce, ‘Har yaushe za ka ƙi ƙasƙantar da kanka a gabana? Ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada.
4
In ka ƙi ka bari su tafi, gobe zan aiko da fāra a ƙasarka.
5
Za su rufe fuskar ƙasar, har da ba za a iya ganin ƙasa ba. Za su cinye ɗan sauran abin da ya rage muku daga ɓarnar ƙanƙara, za su cinye dukan itatuwan da suke girma a gonakinku.
6
Za su cika gidajenka, da na fadawanka, da na dukan Masarawa, abin da iyayenka da kakanninka ba su taɓa gani ba, tun daga ranar da suka sami kansu a duniya, har yă zuwa yau.’ ” Sa’an nan Musa ya juya, ya rabu da Fir’auna.
7
Fadawan Fir’auna suka ce masa, “Har yaushe mutumin nan zai zama mana tarko? Ka bar mutanen su tafi domin su yi wa Ubangiji Allahnsu sujada. Har yanzu ba ka san cewa Masar ta lalace ba?”
8
Sa’an nan aka dawo da Musa da Haruna wurin Fir’auna. Sai ya ce, “Ku tafi, ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada. Amma wa da wa za su tafi?”
9
Musa ya amsa, “Za mu tafi tare da ƙanananmu, da tsofaffinmu, da ’ya’yanmu maza da mata, da kuma garkunanmu na shanu da tumaki, gama dole ne mu yi bikin ga Ubangiji.”
10
Fir’auna ya ce, “Ubangiji ya taimaka bisa ga niyyarku, amma matanku da ƙanananku ba za su tafi ba! A fili yake kuna da niyyar mugunta.
11
Sam! Wannan ba zai taɓa yiwu ba, sai ko maza kaɗai su tafi su yi wa Ubangiji sujada, gama abin da kuke so ke nan.” Sa’an nan aka kori Musa da Haruna daga gaban Fir’auna.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options