Skip to content
Maimaitawar Shari’a 32:19-38

Maimaitawar Shari’a 32:19-38

19
Ubangiji ya ga wannan ya kuma ƙi su, domin ’ya’yansa maza da mata sun husata shi.
20
Ya ce, “Zan ɓoye fuskata daga gare su, in ga ƙarshensu; gama su muguwar tsara ce, ’ya’ya ne marasa aminci.
21
Sun sa ni kishi ta wurin abin da ba allah ba, suka kuma husata ni da gumakansu na wofi. Zan sa su yi kishi ta wurin waɗanda ba mutane ba; zan sa su yi fushi ta wurin al’ummar da ba ta da sani.
22
Gama fushina ya kama wuta, tana ci har ƙurewar zurfin lahira. Za tă cinye duniya da girbinta, tă kuma sa wuta a tussan duwatsu.
23
“Zan tula masifu a kansu in kuma gama kibiyoyina a kansu.
24
Zan aika da yunwa mai tsanani a kansu, zazzaɓi mai zafi da muguwar annoba; zan aika da haƙoran namun jeji a kansu, da dafin mesa masu ja da ciki.
25
Waɗanda suke a waje, takobi zai kashe su, a cikin gidajensu kuma tsoro zai mamaye su. ’Yan maza da ’yan mata za su hallaka, haka ma jarirai da maza masu furfura.
26
Na ce zan watsar da su in sa a manta da su a tunanin ’yan adam.
27
Amma ina tsoron tsokanar abokin gāba, don kada abokan gāba su kāsa ganewa har su ce, ‘Hannunmu ne ya yi nasara; ba Ubangiji ne ya aikata dukan wannan ba.’ ”
28
Al’ummai ne marasa azanci, babu ganewa a cikinsu.
29
A ce su masu hikima ne har su gane wannan su gane abin da ƙarshensu zai zama!
30
Yaya mutum guda zai kore dubu, mutum biyu su sa dubu goma su gudu, sai ko Dutsensu ya sayar da su, sai ko Ubangiji ya bashe su.
31
Gama dutsensu ba kamar Dutsenmu ba ne, abokan gābanmu sun san da haka.
32
Kuringarsu ta fito daga kuringar Sodom ne, daga gonakin Gomorra kuma. ’Ya’yan inabinsu dafi ne, nonnansu masu ɗaci ne.
33
Ruwan inabinsu dafin macizai ne, mugun dafin gamshaƙa ne.
34
“Ban jibge wannan a ma’ajiya na kuma yimƙe shi a taskokina ba?
35
Sakayya nawa ne, zan kuwa ɗau fansa. A cikin lokaci, ƙafarsu za tă yi santsi; ranar masifarsu ta yi kusa hallakarsu kuma tana gaggautawa a kansu.”
36
Ubangiji zai shari’anta mutanensa yă kuma ji tausayin bayinsa sa’ad da ya ga ƙarfinsu ya ƙare babu kowa kuma da ya rage, bawa ko ’yantacce.
37
Zai ce, “To, ina allolinsu, dutsen da suka yi mafaka a ciki,
38
allolin da suka ci kitsen hadayunsu suka kuma sha ruwan inabin hadayunsu? Ku sa su tashi su taimake ku mana! Bari su ba ku mafaka!
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options