Maimaitawar Shari’a 3:1-11
1
Biye da wannan muka juya muka haura ta hanyar wajen Bashan, inda Og, sarkin Bashan tare da dukan mayaƙansa suka fito don su sadu da mu a yaƙi, a Edireyi.
2
Ubangiji ya ce mini, “Kada ka ji tsoronsa, gama na riga na miƙa shi da dukan mayaƙansa da kuma ƙasarsa gare ka. Yi masa abin da ka yi wa Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulkin Heshbon.”
3
Saboda haka Ubangiji Allahnmu ya ba da Og, sarkin Bashan da dukan mayaƙansa a hannuwanmu. Muka karkashe su, ba mu bar wani da rai ba.
4
A wannan lokaci muka kwashe dukan biranensa. Babu ɗaya daga birane sittin da ba mu ɗauke daga gare su ba, dukan yankin Argob, masarautar Og a Bashan.
5
Dukan biranen nan masu katanga da suke da tsayi masu ƙofofi da ƙyamare, akwai kuma manya ƙauyukan da ba su da katanga.
6
Muka hallaka su ƙaƙaf, kamar yadda muka yi wa Sihon sarkin Heshbon, muka hallaka kowace birni, maza, mata da yara.
7
Amma dukan dabbobin da kuma ganimar daga biranensu muka kwaso wa kanmu.
8
A lokacin ne muka ƙwace wannan ƙasa daga hannun sarakunan nan biyu na Amoriyawa, wato, ƙasa wadda take a hayin Urdun, daga Kwarin Arnon zuwa Dutsen Hermon.
9
(Hermon ne Sidoniyawa suke kira Siriyon, Amoriyawa kuwa suna kira shi Senir.)
10
Muka kama dukan biranen da suke kan tudu, da dukan Gileyad, da dukan Bashan, har zuwa Saleka da Edireyi, biranen masarautar Og a Bashan.
11
(Og sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu cikin Refahiyawa. An yi gadonsa da ƙarfe, tsawon gadon ya fi ƙafa goma sha uku, fāɗinsa kuwa ƙafa shida ne. Yana nan a Rabba ta Ammonawa har yanzu.)
Settings