Daniyel 4:1-17
1
Daga sarki Nebukadnezzar. Zuwa ga mutane da al’ummai da kuma kowane yare, da suke zama a duniya. Salama mai yawa ta tabbata a gare ku!
2
Ina murna in shaida muku game da alamu da al’ajabai waɗanda Allah Mafi Ɗaukaka ya yi ta wurina.
3
Alamunsa da girma suke,
4
Ni, Nebukadnezzar, ina zaune a gidana cikin fadata, ina jin daɗi ina bunkasa.
5
Na yi mafarkin da ya ba ni tsoro. A sa’ad da nake kwance a gadona, siffofi da wahayoyi da suka bi ta cikin tunanina sun firgita ni.
6
Don haka na ba da umarni a tattaro dukan masu hikima na Babilon su bayyana a gabana domin su fassara mini mafarkin.
7
Sa’ad da masu sihiri, da masu dabo, da masanan taurari da masu duba suka zo, na faɗa musu mafarkin, amma ba su iya fassarta mini mafarkin ba.
8
A ƙarshe, sai Daniyel ya zo gabana na kuma faɗa masa mafarkin. (Ana ce da shi Belteshazar, wanda aka ba shi sunan allahna kuma ruhun alloli masu tsarki suna a bisansa.)
9
Na ce, “Belteshazar, shugaban masu sihiri, na san ruhun alloli suna a kanka, babu wani asirin da zai fi ƙarfin ganewarka. Ga dai mafarkin da na yi, sai ka fassara mini.
10
Waɗannan su ne wahayin da na gani a lokacin da nake kwance a gadona, na duba, a gabana kuwa ga wani itace a kafe a tsakiyar duniya, yana da tsawo ƙwarai.
11
Itacen ya yi girma ya kuma yi ƙarfi, har tsayinsa ya taɓa sarari sama; ana iya ganinsa a ko’ina a duniya.
12
Ganyayensa suna da kyau, yana da ’ya’ya jingim, abinci kuma domin kowa da kowa. A ƙarƙashinsa namun jeji suke samun wurin hutawa, kuma tsuntsayen sama suna zaune a bisa rassansa; daga cikinsa kowace halitta take cin abinci.
13
“A cikin wahayin da gani sa’ad da nake kwance a kan gadona, Na duba, a gabana kuwa ga wani ɗan saƙo, mai tsarki, yana saukowa daga sama.
14
Sai ya yi kira da babbar murya ya ce, ‘A sare itacen a kuma yayyanka rassansa; a karkaɗe ganyensa a kuma warwatsar da ’ya’yansa. Bari dabbobi su tashi daga ƙarƙashinsa da kuma tsuntsayen da suke a rassansa.
15
Amma a bar kututturen da kuma saiwoyinsa, a daure shi da ƙarfe da kuma tagulla, a bar shi a cikin ƙasa, a cikin ciyayin filaye. “ ‘Bari yă jiƙu da raɓar, bari yă zauna cikin dabbobi tare da tsire-tsiren duniya.
16
Bari a canja tunaninsa irin na mutane a ba shi tunani irin na dabbobi, har sau bakwai su wuce a kansa.
17
“ ‘An sanar da wannan matsayi ne ta bakin ’yan saƙo, masu tsarki ne kuwa suka sanar da hukuncin, domin masu rai su sani Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a bisa kowane mulkin mutane, yakan kuma ba wa duk wanda ya ga dama, yakan sanya talaka yă zama sarki.’
Settings